Labarai
Majalisar Dokokin Jihar Jigawa Ta Isa Gumel A Cigaba Da Ziyarar Gani Da Ido
Shugaban Kwamitin Majalisar Dokokin Jihar Jigawa mai kula da harkokin kananan hukumomi, Alhaji Aminu Zakari, ya ce suna ziyarar gani da ido a kananan hukumomi 27 na jihar ne domin tantance yadda ake aiwatar da kasafin kowane shekara, da tabbatar da daidaito da ci gaban kananan hukumomi.
Ya bayyana haka ne lokacin da ya jagoranci mambobin kwamitin zuwa ziyarar aiki a sakatariyar karamar hukumar Gumel.
A cewarsa, kwamitin na duba takardun gudanarwa da na kudi domin samun sahihan bayanai kan halin da kananan hukumomi ke ciki, tare da tabbatar da bin ka’idoji da dokoki wajen kashe kudaden gwamnati.
Alhaji Aminu Zakari ya jaddada cewa ziyarar ta kuma samar da damar tattaunawa da bangaren zartarwa, majalisar karamar hukuma da jami’an gudanarwa, domin kara hadin kai da kyakkyawar mu’amala a matakin kananan hukumomi.
Ya kara da cewa, kwamitin ya kafa kananan kwamitoci domin duba ayyuka a wuraren da ake gudanarwa, don tabbatar da inganci da kuma adalci wajen rabon ayyukan jin dadin jama’a a dukkan sassan jihar.
Tunda farko, shugaban karamar hukumar Gumel, Malam Muhammad Gako, ya bayyana cewa yana da yakinin wannan ziyara za ta taka muhimmiyar rawa wajen bunkasa ci gaban kananan hukumomi a fadin jihar.
Malam Muhammad Gako ya bukaci al’umma da su ci gaba da mara wa wannan gwamnati baya a kokarinta na aiwatar da manufofi da shirye-shiryen da za su ci gaba da bunkasa jihar.
Usman Muhammad Zaria
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
-
Labarai6 days agoMasu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki
-
Labarai4 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
