Labarai
Cikar Jigawa Shekaru 34: Gwamna Namadi Ya Yabawa Tsoffin Shugabanni
Gwamna Malam Umar Namadi ya yaba wa shugabannin da suka gabata bisa jajircewa da sadaukarwar da suka yi wajen shimfiɗa tubalin ci gaban jihar tun daga shekarar 1991 zuwa yau.
A taron manema labarai da aka gudanar a fadar gwamnatin Dutse, gwamnan ya ce bikin cika shekaru 34 da kafuwar jihar dama ce ta tunawa, tare da murna da kuma sabunta aniyar ci gaban Jigawa.
Ya bayyana cewa jihar ta samu sauyi a fannoni da dama ciki har da noma, ilimi, kiwon lafiya, hanyoyi da ci gaban zamantakewa. A cewarsa, gwamnatinsa za ta ci gaba da kokari kan waɗannan nasarori tare da bullo da sabbin hanyoyi na bunƙasa jihar.
Namadi ya jaddada kudurinsa na aiwatar da manufofin gwamnatinsa 12, wadanda suka haɗa da samar da ayyukan yi, haɓaka noma, inganta kiwon lafiya da ilimi, da kuma raya ababen more rayuwa.
Ya ce gwamnati ta kaddamar da manyan shirye-shirye a fannoni da dama ciki har da injinan noma, ilimi, kiwon lafiya, hanyoyi da kuma tallafa wa matasa, domin inganta hidima da tabbatar da kyakkyawan shugabanci.
Gwamnan ya yi kira ga al’ummar jihar da su haɗa hannu wajen tabbatar da zaman lafiya da ci gaban jihar, yana mai cewa “Ci gaban Jigawa alhaki ne na kowa.”
Ya tabbatar wa jama’a cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da inganta tattalin arziki, samar da ayyukan yi, da jinƙai, domin rage talauci da inganta rayuwar jama’a.
A ƙarshe, Gwamna Namadi ya gode wa jama’ar Jigawa bisa goyon bayan da suke ba shi, yana mai alƙawarin cewa gwamnatinsa za ta kasance mai gaskiya da rikon amana akoda yaushe.
Usman Muhammad Zaria
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai7 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai7 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai7 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Labarai7 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
-
Labarai7 days agoMasu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki
-
Labarai5 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
