Labarai
Gwamna Namadi Ya Kaddamar Da Gina Titi Mai Nisan Kilomita 35 A Karamar Hukumar Jahun
Gwamnatin Jihar Jigawa ta sake jaddada kudurinta na rage wa manoma wahalhalu wajen jigilar amfanin gonakinsu zuwa kasuwanni mafi kusa a fadin jihar.
Gwamna Umar Namadi ne ya bayyana hakan yayin kaddamar da aikin gina titi kimanin kilomita 35 daga Kwanar Idonduna, Kadowawa, Gangawa zuwa Kwanar Olayinka a karamar hukumar Jahun.

A cewarsa, an bai wa wani kamfani aikin a kan kudi Naira Biliyan 12 da miliyan 900 tare da wa’adin watanni 24.

Gwamnan ya kara da cewa samar da hanyoyin shiga da fita na nufin inganta sufuri na jama’a da kayayyaki da kuma rage radadin da manoma ke fuskanta.

Ya bayyana cewa wannan gwamnati ta kammala tituna 25 daga cikin 26 da ta gada daga gwamnatin da ta gabata.

Namadi ya kara da cewa titin Kwanar Idonduna yana daga cikin tituna 47 da wannan gwamnati ta bayar da kwangilar gina su a kan kudi sama da Naira Biliyan 300.

Shi ma da yake jawabi, Kwamishinan Ayyuka da Sufuri na jihar, Injiniya Gambo S. Malam, ya ce gwamnatin jihar tana ci gaba da gina titunan cikin gari a Aujara a kan kudi Naira Biliyan 3 da miliyan 400.

Ya kara da bayyana cewa, gwamnatin jihar tana kuma aikin gina hanyoyin kauyuka a matsayin wani bangare na kokarin inganta matsayin tattalin arzikin al’ummomin karkara.
Usman Muhammad Zaria
-
Ilimi6 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
-
Labarai1 day ago
Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu
-
Labarai1 day ago
NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta
