Labarai
Majalisar Dokokin Jihar Jigawa Ta Sha Alwashin Inganta Kwazon Kananan Hukumomin Jihar
Majalisar Dokokin Jihar Jigawa ta jaddada kudurin ta na bada managartan shawarwari da za su yi wa kananan hukumomin jihar jagoranci wajen gudanar da ayyukan su kamar yadda yakamata.
Shugaban Kwamatin Kananan Hukumomi na Majalisar, Alhaji Aminu Zakari, ya bada wannan tabbacin lokacin rangadin kwamatin majalisar a sakatariyar karamar hukumar Birniwa.
Alhaji Aminu Zakari Wanda shi ne wakilin mazabar Gwiwa, yace ziyarar Kwamatin na daga nauyin da aka dorawa bangaren majalisa wajen bibiyar yadda Gwamnati ta ke aiwatar da manufofi da shirye shirye domin tabbatar da shugabanci nagari.
Alhaji Aminu Zakari yace haka kuma Kwamatin yana la’akari da batun zamantakewar jama’ar da tattalin arziki a matsayin ma’aunin ci gaban rayuwa da koma bayana domin baiwa bangaren zartaswa shawarwari dan bullo da manufofi da shirye shiryen da za su dace da bukatun Jama’a.
Yace , ziyarar na bada damar ganawa da bangaren zartaswa da na kansiloli da ma’aikata domin tabbatar da tsarin aiki tare ta hanyar kyakkyawar fahimtar juna.
A daya bangaren kuma, kananan kwamitocin da Babban Kwamatin kananan hukumomi na majalisar dokokin jihar Jigawan ya kafa, sun sami nasarar tantance ayyukan raya kasa da karamar hukumar Birniwa ta gudanar a sassan yankin daga watan Oktobar 2024 kawo yanzu.
Karamin Kwamati na daya, bisa jagorancin wakilin mazabar Alhaji Muhammad Abubakar Sa’id ya duba aikin Masallacin kamsissalawati na Kakori, da gyaran masallacin juma’a na Malandi, da sanya fitilu masu amfani da hasken rana a Taljari da shaguna da rumfuna a kasuwar Birniwa da wasu muhimman wurare da suka hada da gyaran gidajen karamar hukumar da gyaran kotun shari’a a Birniwa.
Karamin Kwamati na biyu bisa jagorancin wakilin mazabar Guri, Alhaji Usman Abdullahi Tura Musari, ya duba aikin gina shago guda biyar a bakin Babban titin garin Birniwa da shaguna da rumfuna da cikon kasa a garin Kupsa da masallacin kamsissalawati a kauyen Garuba.
Kazalika, ziyarar Kwamatin ta duba batun daukar malaman duba gari 22 da Gina ajujuwa a makarantun ‘Yayan fulani.
Tunda farko, shugaban karamar hukumar Birniwa, Malam Shehu Baba Birniwa, ya bayyana aniyarsa ta aiki da shawarwarin Kwamatin domin cigaban karamar hukumar sa.
Malam Shehu Baba ya ce tun daga kama mulkinsa ya bar kofar sa a bude da nufin cusa dabi’ar aiki tare da masu ruwa da tsaki a matsayin turba mai sauki wajen gudanar da mulkin karamar hukumar.
Usman Mohammed Zaria
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai7 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai7 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Labarai7 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
-
Labarai7 days agoMasu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki
-
Labarai5 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
