Labarai
Mai Martaba Sarkin Dutse Ya Kaddamar Da Rabon Zakka Ta Shekarar 1446
Mai Martaba Sarkin Dutse, Dr Hameem Nuhu Muhammadu Sunusi ya kaddamar da rabon zakkar kudi ta shekarar musulunci ta 1446 a gundumar Yayari dake Karamar Hukumar Buji.
A jawabin sa, Mai Martaba Sarkin ya ja hankalin al’umma da su ci gaba da fitar da hakkin Allah domin samun makoma a nan duniya da kuma gobe kiyama.

Ya nuna gamsuwa da nasarorin da Gundumar ta samu wajen tattara zakka a masarautar sa.
Daga bisani ya karrama Hakimin Yayari, Alhaji Garba Muhammad da Dagaci da kuma Mai Unguwar cikin garin Yayari.

A jawabin sa, Sa’in Dutse, Mallam Mahmud Yunusa yace gundumar Yayari ce ta zo na 1 a tattara zakkar kudi yayin da Gundumomin Gantsa da Fagam suka zo na 2 da na 3.
Ya ce an raba zakkar fiye da naira miliyan goma ga mutane 300, inda wasu suka sami zakkar naira dubu 20 zuwa naira dubu 35.

A jawabin sa, shugaban Karamar Hukumar Buji Najibullah Falalu Tukur Gantsa yace Karamar Hukumar zata ci gaba da hadin kai da gundumar Yayari da sauran gundumomin hakimanta wajen ganin Karamar Hukumar ta rike matsayinta na ja gaba wajen tattara zakka.
Ya kuma yabawa mai Martaba Sarkin Dutse bisa jajircewar sa wajen ganin al’umma suna fitar da hakkin Allah.

Mai martaba sarki ya samu rakiyar Galadiman Dutse da sauran ‘yan majalissar Sarki.
Usman Mohammed Zaria
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai7 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai7 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Labarai7 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
-
Labarai7 days agoMasu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki
-
Labarai5 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
