Labarai
Gwamnan Zamfara Na Nan Daram A PDP – Dantawasa
Gwamnatin jihar Zamfara ta musanta ikirarin da ke yawo a wasu bangarori na cewa, Gwamna Dauda Lawal na shirin sauya sheka zuwa jam’iyyar APC, yana mai bayyana jita-jitan a matsayin maras tushe, balle makama, kuma aikin ‘yan adawa ne.
A wata sanarwa da kwamishinan yada labarai da al’adu na jihar, Mahmud Muhammad Dantawasa ya fitar, ya ce wasu mutane ne da ke neman a ci gaba da damawa da s uke yawo da wannan zancen bayan da jama’a sun ki amincewa da wannan labarin.
Sanarwar ta bayyana wannan jita-jita a matsayin karya, abin dariya, da kuma matsanancin yunƙuri na ƴan adawa da ke hasken s uke dushewa.
Ta ce yadda Gwamna Lawal ya samu sauyi da jajircewarsa na sake gina Zamfara ya sa ya samu karbuwa sosai, har ma da abokan hamayyar siyasa.
“Ba abin mamaki ba ne cewa ‘yan jam’iyyar APC, musamman wadanda suka haddasa rugujewar shekara da shekaru a Zamfara, suna zawarcin Gwamna Lawal.
“Amma a fayyace cewa shi dan jam’iyyar PDP ne, mutum ne mai kishin kasa wanda ba zai yi watsi da jam’iyyar da ta ba shi ikon ceto jihar ba, ko da kuwa wace irin jarabawar ce ake fuskanta.”
Sanarwar ta kuma bayyana cewa, Gwamna Lawal na kan hanyarsa ta zuwa Abuja ne domin halartar taron kwamitin zartarwa na jam’iyyar PDP na kasa (NEC), inda ya jaddada kudirinsa na tabbatar da kimar jam’iyyar da manufofinta.
REL/AMINU DALHATU.
-
Labarai3 days agoIran ta Tabbatar da Kisan Ayatollah Khamenei a Hare-haren Amurka da Isra’ila
-
Labarai4 days agoMajalisar Dokokin Jihar Kaduna Ta Amince da Kasafin Kudin Kananan Hukumomin Jihar na 2026
-
Labarai4 days agoAzumin Ramadan: Shugaban Karamar Hukumar Birnin Kudu Ya Bada Tallafin Kudi ga Marasa Galihu
-
Labarai6 days agoUwargidan Gwamnan Zamfara Ta Kaddamar da Rabon Tallafin Ramadan ga Marasa Galihu
-
Labarai6 days agoWani Bam Kirar Hannu Ya Fashe a Kan Hanyar Gusau Zuwa Funtua
-
Labarai3 days agoBankin Raya Kasashen Afirka Zai Samar da Shirin Bunƙasa Aikin Noma a Jigawa
-
Labarai3 days agoGwamnatin Jigawa ta Gargadi ‘Yan Kwangila Kan Ingancin Abincin Ramadan
-
Labarai3 days agoMasarautar Hadejia ta Raba Zakkar Kayan Amfanin Gona da Dabbobi a Garin Unik
