Labarai
Zabe Babu Hamayya: Isma’il Dutse Ya Karbi Ragamar NUJ Jigawa
An zabi Comrade Isma’il Ibrahim Dutse na ma’aikatar yada labarai a matsayin sabon shugaban kungiyar ‘yan jaridu NUJ ta kasa reshen jihar Jigawa ba tare da hamayya ba.
A lokacin da yake sanar da sakamakon zaben, mataimakin shugaban kungiyar na kasa mai kula da shiyya ta daya wato Zone A, Comrade Tukur Umar Muhammad ya ce an kuma zabi Nura Sani Bello da Najib Umar da Aminu Umar Shuwajo ba tare da hamayya ba.

Tukur ya ce Aisha Abba Ahmed ta kamfanin dillancin labarai na kasa NAN dake Dutse ta samu nasara da yawan kuri’u 46, shi kuma Abdullahi Mukhtar ya sami kuri’u 34, yayin da Larai Musa na NTA ta sami kuri’u 14.

Tukur Umar, ya bayyana Aisha Abba Ahmed a matsayin wacce ta sami nasara a zaben da ta zamo sakatariyar kungiyar NUJ a jihar Jigawa.
Kazalika, Auwal Muhammad Kazaure ya samu nasara da kuri’u 69 akan Habibu Yusuf Adamu Babura wadda ya sami kuri’u 27.


A don haka, Mataimakin Shugaban na NUJ ya bayyana Auwal Muhammad Kazaure a matsayin ma’ajin kungiyar.
Sakataren kungiyar na shiyyar Zone A, Comrade Abdulrazak Bello Kaura ne ya rantsar da sabbin shugabannin nan take.



A jawabinsa, sabon shugaban kungiyar NUJ reshen jihar Jigawa, Isma’il Ibrahim Dutse ya bayyana zaben sa ba tare da hamayya ba a matsayin wani babban karimci da aka nuna masa.
Ya kuma yabawa masu ruwa da tsaki ciki har da Gwamna Umar Namadi bisa gudummawar da su ka bayar wajen samun nasarar zaben da aka gudanar cikin kwanciyar hankali da lumana.


Wakilinmu ya aiko mana da rahoton cewar, wadanda su ka halarci taron, sun hada da kwamishinan yada labarai, al’adu da matasa, Alhaji Sagir Musa Ahmed, da tsoffin shugabannin kungiyar, Alhaji Sabo Abdullahi Guri da Alhaji Mati Ali da wakilan sakataren Gwamnati da na shugaban ma’aikata da kuma Shugaban gidan Radiyon Tarayya Horizon FM, Dr Musa Idris Barnawa.


Kungiyar dai ta gudanar da taro karo na 8 wanda ya wakana a sakatariyar kungiyar da ke Dutse, babban birnin jihar.
Bayan kammala zaben, Shugabannin Kungiyar ta kasa, sun kai ziyarar ban girma gidan gwamnatin jihar domin gabatar da sabbin shugabannin kungiyar na jihar ga babban jami’in yada labarai na Gwamnan Jihar, Hamisu Mohammed Gumel.
Usman Mohammed Zaria
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
-
Labarai6 days agoMasu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki
