Labarai
Gwamna Namadi Ya Kaddamar Da Masallacin Juma’a A Garin Samamiya Da Ke Birnin Kudu
Gwamnatin Jihar Jigawa ta ce za ta duba yiwuwar inganta cibiyar lafiya tare da kafa makarantar sakandare a garin Samamiya da ke karamar hukumar Birnin Kudu.

Gwamna Umar Namadi ya bayyana haka a lokacin kaddamar da sabon masallacin Juma’a da gidan marayu da makarantar islamiyya, wanda dan asalin yankin Alhaji Muhammad Abubakar Samamiya ya gina a matsayin wakafi ga mahaifinsa.

Malam Umar Namadi ya bayyana jin dadinsa bisa wannan kokari na Alhaji Muhammad Abubakar Samamiya.

Ya kuma bukaci masu hannu da shuni da su yi koyi da wannan matakin domin amfanin talakawa da marasa galihu a cikin al’umma.

Ya jaddada aniyar gwamnatin jihar na ci gaba da yin aiki kafada da kafada da irin wadannan mutane a cikin al’umma.

Rediyon Najeriya ya ruwaito cewa, Gwamna Umar Namadi tare da rakiyar sakataren gwamnatin jihar Malam Bala Ibrahim, da ‘yan majalisar zartarwa na jiha, da shugaban karamar hukumar Birnin Kudu da sauran manyan baki sun yi sallar Juma’a a sabon masallacin Abubakar Samamiya da ke karamar hukumar Birnin Kudu.
Usman Muhammad Zaria
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
-
Labarai6 days agoMasu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki
-
Labarai4 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
