Connect with us

Ilimi

Ilimi Tsanin Kaiwa Ne Ga Nasara – Gwamana Dauda Lawal

Published

on

Gwamnan jihar Zamfara Dauda Lawal ya bayyana ilimi a matsayin wani tsani, matakala ta kaiwa ga samun duk wani abin nema a duniyar nan.

Gwamnan ya halarci taron yaye ɗalibai karo na uku da na huɗu na Jami’ar tarayya, wanda ya gudana a filin taro na Jami’ar da ke Gusau a jiya Asabar.

Mai magana da yawun gwamnan, Sulaiman Bala Idris ya bayyana a cikin wata sanarwa da ya fitar yau a Gusau cewa, Gwamna Lawal ya shelanta bayar da gurbin karatu ga duk wanda ya zo na ɗaya a Jami’ar.

Cikin jawabin sa a wurin taron, Gwamnan ya yaba wa shugabannin Jami’ar game da yadda suka iya ririta ɗan abin da suke da shi, duk da ɗimbin ƙalubalen da suke fuskanta.

Ya ce, “Ina matuƙar farin cikin kasancewa da ku yau a wannan bikin yaye ɗalibai karo na uku da na huɗu a wannan jajirtacciyar Jami’a, Jami’ar gwamnatin tarayya ta Gusau. Ina taya jami’ar nan murnar samun wannan nasara, duk kuwa da matsalolin da suke fuskanta tun lokacin da aka kafa ta. Ina kuma yaba wa iyaye da ɗalibai bisa sadaukarwar da suka nuna har zuwa wannan matsayi.

Muna sa ran samun makoma mai kyau kuma mai albarka duk da tarin ƙalubalen da muke fuskanta a matsayinmu na jiha kuma al’umma. Muna yin addu’a kuma muna aiki ba dare ba rana don samar da makoma mai kyau. Duk waɗannan matsaloli za su wuce da izinin Allah Maɗaukakin Sarki.”

Gwamnan ya yi ƙarin haske kan ƙoƙarin gwamnatinsa na gyara harkar ilimi a Jihar Zamfara bayan kafa dokar ta-ɓaci a bara.

“A matsayinmu na gwamnati, mun ƙuduri aniyar ilimantar da duk ’ya’yan Zamfara. Ilimi shi ne ginshiƙin da ke haskaka ruyuwar ɗan adam.

“Mun ware maƙudan kuɗaɗe ga ɓangaren ilimi a cikin kasafin kuɗinmu na 2024 kuma muna fatan za mu kai ga babban matsayi a 2025, 2026, da 2027. Muna fatan cimma kashi 25 zuwa 30 na haɓaka tsarin ilimi. Tare da samar da ingantaccen tsari a fannin da sarrafa albarkatun da ya ƙunsa, muna da ƙwarin gwiwar cewa za mu farfaɗo da ababen more rayuwa, ɗaukar ƙwararrun malamai, horarwa da sake horar da waɗanda ake da su.

“Za kuma mu ƙara yawan masu karatu a makarantun firamare da na gaba da firamare ta hanyar wayar da kan jama’a da samar da ingantattun wuraren koyo da koyarwa. Ilimi kyauta ne, kuma muna fatan ya zama wajibi ga kowa.

“Mun kuma yi wa manyan makarantunmu da ke jihar kason kuɗi mai yawa don fara aikin gyara su zuwa matakai masu inganci. A karon farko Jami’ar Jihar Zamfara na shirye-shiryen amincewa da shirin Hukumar Kula da Jami’o’i ta Ƙasa. Mun umurci ’yan kwangilar da gwamnatin da ta shuɗe ta tilastawa barin wuraren aiki da su koma bakin aiki, kuma muna fatan nan da watanni masu zuwa, rukunin dindindin na jami’ar zai fara aiki. A lokaci guda, NUC za ta amince ga duk kwasa-kwasai.

“Mun karɓi mulki a jihar da gwamnati ta ƙi biyan kuɗaɗen jarrabawar WEAC da NECO har na biliyoyin Naira fiye da shekaru uku. Dole muka yi shiri na musamman da hukumomin, kuma tun daga lokacin an fara biyan kuɗi a kan kari kuma za a kammala su a kan lokaci.

“A cikin ƙarancin albarkatunmu, za mu ci gaba da bayar da taimako ga jami’a. Burinmu shi ne mu ƙara haɓaka ilimi a jiharmu ta yadda za a samu damarmaki ga ɗaukacin matasanmu da za a horar da su don kai ga ƙololuwar da ilimi ke samarwa.”

Dutsinma/Wababe

Labarai

Labarai8 hours ago

Hukumar Kula da Kogin Benuwe ta Dauki Matakin Yashe Laka da Yashi da ke Barazana ga Noman Rani

Ayyukan ban ruwa a yankin Kogin Benuwe na fuskantar barazana sakamakon taruwar Laka da Yashi a kogin, lamarin da ke...

Labarai1 day ago

Gwamna Namadi Ya Raba Tallafin Ramadan ga Ma’aikata da Marasa Galihu

Daga Usman Muhammad Zaria Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya raba tallafin kayan abinci na watan Ramadan tare da...

Labarai1 day ago

Sojoji Sun Yi Nasarar Kwato Dabbobi 257 da Aka Sace a Karamar Hukumar Gwarzo

Daga Abdullahi Jalaluddeen Sojojin Najeriya sun sami nasarar dawo da Shanu da Awaki  257 da aka sata a  wani aikin...

Labarai1 day ago

Uwargidan Gwamnan Zamfara ta Yaba da Yadda Aka yi Rabon Tallafin Ramadan

Daga Aminu Dalhatu  Uwargidan Gwamnan Jihar Zamfara, Hajiya Huriyya Dauda Lawal, ta yaba wa dukkan masu ruwa da tsaki bisa...

Labarai1 day ago

Gwamnatin Kebbi Za ta Raba Hatsi da Kayayyakin Aikin Gona ga Marasa Galihu

Daga Sani Dutsinma Gwamnatin Jihar Kebbi ta kammala shirye-shiryen raba kayayyakin aikin noma da nau’o’in hatsi daban-daban ga mutane miliyan...

Labarai2 days ago

Gwamnatin Kwara Ta Jaddada Kudurinta Na Kula Da Jin Daɗin Masu Harkar Sufuri

Gwamnatin Jihar Kwara ta bai wa masu harkar sufuri a jihar tabbacin ci gaba da kare muradunsu da jin daɗinsu....

Labarai2 days ago

Gwamnan Zamfara Ya Haramta Karbar Kudin Haraji A Hannu

Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya bayar da umarnin dakatar da duk wani tsarin karbar kuɗaɗen shiga ta tsabar kuɗi...

Labarai2 days ago

Gwamnatin Tarayya Ta Faɗaɗa Rijistar Tallafin Jama’a Domin Tantance Masu Buƙata

Gwamnatin Tarayya na faɗaɗa tare da ƙarfafa Rijistar Tallafin Jama’a ta Ƙasa National Social Register domin tabbatar da cewa an...

Labarai2 days ago

Gwamna Idris Ya Ba da Umarnin Binciken Gobarar da Ta Tashi a Makarantar Nurul Haqq da ke Birnin Kebbi

Gwamnan Jihar Kebbi, Nasir Idris, ya bayar da umarnin gaggauta kafa wani kwamitin bincike mai ƙarfi domin gano musabbabin gobarar...

Labarai2 days ago

Taraba Ta Kaddamar da Rarraba Kayan Aikin A Kananan Hukumomi 16

Hukumar Kula da Ci gaban Kiwon Lafiyar Matakin Farko ta Jihar Taraba ƙarƙashin Shirin IMPACT, ta ƙaddamar da rarraba kayan...

Mafi Shahara