Labarai
Gwamna Abba Kabir Ya Mayar Da Muhammadu Sanusi II Kan Muƙamin Sarkin Kano
Gwamnan Jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya sanar da mayar da Muhammadu Sanusi II a matsayin sarkin Kano.
Gwamna ya bayyana hakan ne ga manema labarai jim kaɗan bayan sanya hannu kan dokar da ta yi gyara ga dokar da ta kafa dokar masarautun Kano ta 2019.
Ya ce an yi hakan ne da nufin dawo da martabar masarautar ta Kano.
A yau Alhamis ne Majalisar dokoki ta jihar Kano ta yi wa ƙudurin dokar soke masarautu biyar na Kano – wato Kano, Bichi, Rano, Karaye da Gaya karatu na uku tare da amincewa da ita.
Daga nan ne aka miƙa dokar ga gwamnan wanda ya sanya mata hannu.
A lokacin jawabin da ya yi, Gwamna Kabir ya ce: “Bayan soke dokar masarautu ta jihar Kano ta 2019, hakan na nufin cewa masarautar Kano ta koma matsayinta gabanin dokar ta 2019”.
Ya ƙara da cewa “hakan na nufin babu wani halastaccen sarki a Kano face Sarki Muhammadu Sunusi”.
Gwamnan ya umarci dukkan sarakunan da lamarin ya shafa da su bar gidajen sarautun tare da mika kayan gwamnati da ke hannunsu cikin kwanaki 2 ga kwamishinan kananan hukumomi da masarautu.
Ya kuma bai wa al’ummar jihar tabbacin cewa gwamnatinsa ta himmatu wajen ganin an zauna lafiya, sannan ya bukaci jama’a da su rika gudanar da harkokinsu cikin kwanciyar hankali.
Abdullahi Jalaluddeen
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
-
Labarai6 days agoMasu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki
-
Labarai4 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
