Connect with us

Fasaha

Majalisar Wakilai Za Ta Gayyaci Ministan Lafiya Ya Mata Bayani

Published

on

Majalisar wakilai za ta gayyaci ministan lafiya domin yiwa ‘yan Najeriya bayani kan yanayin da ya kai ga rashin aiwatar da ayyukan jinya kyauta ga mata masu juna biyu da da kuma bayan haihuwa.

Matakin dai ya biyo bayan kudirin da dan majalisa daga jihar Bauchi Alh Mohammed Dan Abba Shehu ya gabatar a zaman majalisar.

Da yake gabatar da kudirin, Alhaji Dan Abba Shehu, ya bayyana cewa gwamnati na ware kudade a cikin kasafin kudin shekara na cibiyoyin kula da lafiyar jama’a domin samar da ayyukan kiwon lafiya ga ‘yan kasa musamman mata masu juna biyu wadanda iyalansu ba sa iya samun magani

Dan majalisar wanda ya jaddada mahimmancin tsarin kiwon lafiya kyauta ga talakawan Najeriya, ya jaddada bukatar gwamnati ta ba da fifikon ayyukan da suka dace don baiwa mata masu juna biyu damar samun magani kyauta daga Cibiyar Kiwon Lafiyar Jama’a a lokacin haihuwa.

Ya bayyana damuwarsa cewa har yanzu Najeriya na fama da yawaitar cututtuka da ke haifar da mace-macen mata masu juna biyu a duk shekara.

Alhaji Dan Abba Shehu, ya jaddada cewa rashin kulawar gwamnati na bukatar cibiyoyin kiwon lafiyar jama’a su samu kwararrun likitocin su ba da kulawar da ta dace ga marasa lafiya ciki har da mata masu juna biyu a lokacin haihuwa domin magance matsalar.rikitarwa da kuma nemo mafita na dindindin ga barazanar.

Yayin da majalisar ta amince da kudirin, ta umarci kwamitinta na cibiyoyin kiwon lafiya da ya tabbatar da bin kudurorin.

COV: TSIBIRI/Wababe

Labarai

Labarai21 hours ago

Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu

Daga Nasir Malali  Dakarun Sashe na biyu na Rundunar Haɗin Gwiwa ta Arewa maso Yamma, Operation FANSAN YAMMA, sun ceto...

Labarai23 hours ago

NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta

Daga Yusuf Zubairu, Kaduna Hukumar Raya Yankin Arewa Maso Yamma ta bayyana dawo da tsaro a matsayin babban fifikonta a...

Labarai5 days ago

Gwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, zai halarci zama na 81 na Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya...

Ilimi6 days ago

An Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo

Daga Khadijah Aliyu  Karamar Hukumar Gwarzo ta Jihar Kano ta raba kayan makaranta guda 20,243 ga ɗaliban makarantun firamare daban-daban...

Labarai1 week ago

Gwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027

Daga Usman Muhammad Zaria  Gwamnatin Jihar Jigawa ta sake jaddada aniyarta ta ci gaba da aiki kafada da kafada da...

Labarai1 week ago

Mataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya

Daga Bello Wakili, Abuja Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya dawo Najeriya bayan ya wakilci Shugaba Bola Ahmed Tinubu a...

Labarai1 week ago

UNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina

Daga Isma’il Adamu, Katsina Asusun Tallafawa Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya, UNICEF, tare da haɗin gwiwar Hukumar Ilimin Firamare ta...

Labarai1 week ago

NSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Hukumar Tsaro Farin kaya ta Najeriya, NSCDC, reshen Jihar Zamfara, ta kama wani mutum mai shekaru...

Labarai1 week ago

Majalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari

Daga KHADIJAH ALIYU, Kano Majalisar Dokokin Jihar Kano ta yi kira ga gwamnatin jihar da ta tabbatar da kammala aikin...

Labarai1 week ago

Masu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki

Daga ALI MUHAMMAD RABIU Shirin Ƙarfafa Juriya Ga Sauyin Yanayi A Yankunan Busassun yankuna na Jihar Kwara, KWACReSAL, ya fara...

Mafi Shahara