Kasuwanci
Zamfara Zata Fara Biya Mafi Karancin Albashi Na Dubu 30.

Gwamna Dauda Lawal na jihar Zamfara ya bayyana cewa gwamnatinsa za ta fara biyan mafi karancin albashi na naira 30,000 daga wata mai zuwa.
Gwamnan ya bayyana hakan ne a wata ganawa da ya yi da shugabannin kungiyar kwadago ta Najeriya NLC reshen jihar Zamfara.
A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan jihar, Sulaiman Bala Idris ya fitar, ya bayyana cewa aiwatar da mafi karancin albashin na nuni da kudirin gwamnatin jihar na inganta jin dadin ma’aikata.
A cewar sanarwar, gwamnatin jihar za ta fara biyan mafi karancin albashi na (30,000) Naira dubu talatin maimakon Naira dubu bakwai (7,000) daga watan Yunin bana.
Yayin da yake jawabi ga shugabannin kungiyar kwadago ta Najeriya NLC da TUC reshen jihar Zamfara, Gwamna Lawal ya jaddada cewa, aiwatar da mafi karancin albashi na Naira dubu talatin da nufin zaburar da ma’aikatan Zamfara.
“Tun lokacin da na hau kujerar gwamnan jihar Zamfara, gwamnatina ta aiwatar da sauye-sauye da dama na ma’aikatan gwamnati domin tabbatar da walwalar ma’aikata.
“Mun samu nasarar biyan albashin ma’aikata na watanni uku da aka hana, biyan kudin hutu, da sauran alawus-alawus.
Gwamna Dauda ya ci gaba da bayanin cewa, gwamnatin sa ta biya jimillar Naira biliyan 4,337,087,490 a cikin bagagi hudu ga wadanda suka yi ritaya daga jiha da kananan hukumomi, wadanda ba a biya su albashi ba tun shekarar 2011.
Ya kara da cewa, akwai tsare-tsare na inganta ayyukan ma’aikatan gwamnati a jihar, ya kara da cewa, babu wani ma’aikaci da ya kamata ya damu da yin ritaya, domin za mu tabbatar da biyan kudaden fansho a kan kari ba tare da bata lokaci ba, domin mun himmatu wajen gudanar da aikin ceto.
REL/ SANI DUTSINMA/\Wababe
-
Labarai3 days agoIran ta Tabbatar da Kisan Ayatollah Khamenei a Hare-haren Amurka da Isra’ila
-
Labarai4 days agoMajalisar Dokokin Jihar Kaduna Ta Amince da Kasafin Kudin Kananan Hukumomin Jihar na 2026
-
Labarai4 days agoAzumin Ramadan: Shugaban Karamar Hukumar Birnin Kudu Ya Bada Tallafin Kudi ga Marasa Galihu
-
Labarai6 days agoUwargidan Gwamnan Zamfara Ta Kaddamar da Rabon Tallafin Ramadan ga Marasa Galihu
-
Labarai6 days agoWani Bam Kirar Hannu Ya Fashe a Kan Hanyar Gusau Zuwa Funtua
-
Labarai3 days agoBankin Raya Kasashen Afirka Zai Samar da Shirin Bunƙasa Aikin Noma a Jigawa
-
Labarai3 days agoGwamnatin Jigawa ta Gargadi ‘Yan Kwangila Kan Ingancin Abincin Ramadan
-
Labarai3 days agoMasarautar Hadejia ta Raba Zakkar Kayan Amfanin Gona da Dabbobi a Garin Unik
