Labarai
Hukumar Alhazai Ta Kaduna Ta Kira Ga Sabbin Mambobinta Su Tabbatar da Nasarar Hajjin Bana
Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Kaduna ta yi kira ga sabbin mambobinta biyu na Kwamitin Musamman na Hajji da su yi amfani da irin gagarumar kwarewarsu domin tabbatar da nasarar aikin Hajjin bana.
Shugaban hukumar, Malam Salihu Abubakar, ya yi wannan kiran ne a yayin da yake jawabi ga Sabbin mambobin Kwamitin Sheikh Halliru Abdullahi Maraya da Malam Abdullahi Bayero da ya gudana a dakin taron hukumar da ke Kaduna.
Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Uba Sani, shine ya amince da nadin Sheikh Halliru Abdullahi Maraya da Malam Abdullahi Bayero a matsayin mambobin Kwamiti na Musamman na aikin Hajji a Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Kaduna.
Yayin da yake masu jawabi, Shugaban Hukumar, Malam Salihu Abubakar ya yaba da kwarewarasu akan aikin hajji tareda janyo hankalinsu na mahimmancin dake akwai na cigaba da bada gudunmuwa domin nasarar aikin Hajji wannan shekaran da Kuma wasu masu zuwa.
Har ila yau, ya bayyana cewa jimillar maniyyata 3,409 daga Jihar Kaduna suka kammala biyan kudin aikin Hajji wannan shekarar kafin wa’adin da Hukumar Hajji ta Kasa ta gindaya.
Da yake jawabi, daya daga cikin Sabin mabobin Kwamitin Sheikh Halliru Abdullahi Maraya ya nuna godiya bisa damar da aka ba su na hidima ga bakin Allah tare da alkawarin ba da gudunmawa don tabbatar da nasarar aikin Hajjin bana.
Haka zalika, shima daya daga cikin Sabin mabobin Kwamitin, Malam Abdullahi Bayero ya gode wa Gwamna Uba Sani bisa amincewa da su da yayi na basu wannan damar kara yiwa bakin Allah hudima, tare da yin addu’ar samun nasarar aikin Hajji baki daya.
Dukkan sabbin mambobin kwamitin, kwararu ne da suka dade suna bada gudunmuwa don cigaban aikin hajji da kuma addinin musulunci a Jihar Kaduna dama kasa baki daya.
Cov/Adamu Yusuf
-
Labarai3 days agoIran ta Tabbatar da Kisan Ayatollah Khamenei a Hare-haren Amurka da Isra’ila
-
Labarai4 days agoMajalisar Dokokin Jihar Kaduna Ta Amince da Kasafin Kudin Kananan Hukumomin Jihar na 2026
-
Labarai4 days agoAzumin Ramadan: Shugaban Karamar Hukumar Birnin Kudu Ya Bada Tallafin Kudi ga Marasa Galihu
-
Labarai6 days agoUwargidan Gwamnan Zamfara Ta Kaddamar da Rabon Tallafin Ramadan ga Marasa Galihu
-
Labarai6 days agoWani Bam Kirar Hannu Ya Fashe a Kan Hanyar Gusau Zuwa Funtua
-
Labarai3 days agoBankin Raya Kasashen Afirka Zai Samar da Shirin Bunƙasa Aikin Noma a Jigawa
-
Labarai3 days agoGwamnatin Jigawa ta Gargadi ‘Yan Kwangila Kan Ingancin Abincin Ramadan
-
Labarai3 days agoMasarautar Hadejia ta Raba Zakkar Kayan Amfanin Gona da Dabbobi a Garin Unik
