Kasuwanci
Za Mu Taimaka Wajen Bunkasa Noma- Hon. Mustapha

Shugaban kwamitin majalisar dattijai mai kula da ayyukan noma da raya karkara, Sanata Saliu Mustapha, ya Jaddada kudirinsa na tallafama yunkurin gwamnatin tarayya wajen bunkasa sashen noma don Samar da sana’o’i da wadata kasa da abinci.
Sanatan ay bayyana hakan ne yayi da yake kaddamar da rabon taki buhu 3,500 ga kananan manoma a da suka fito daga kananan hukumomi hudu dake mazabarsa ta Kwara ta tsakiya a Jihar Kwara.
Sanatan Salihu Mustapha, ya ce rabon kayan noman da suka hada da injection nan ban ruwa wani yunkuri ne a matakin farko na tabbatar da dorewar ayyukan noma a fadin gundumar dama Jihar baki daya.
Sanatan ya kara da cewa wadanda aka tsara suci gajiyar rabon kayan sun hada da mambobin kungiyar manoma ta Najeriya wato AFAN, mambobin kungiyoyin manoma na jam’iyyar APC da daidaikun jama’a dake sana’ar noma a mazabar tasa.
Da yake kaddamar da rabon kayayyakin noman a filin wasa na hukumar raya kogin Neja ta karamar hukumar Ilorin, Sanata Mustapha, ya ce akwai tunanin fadada shirin don ganin wasu karin manoma sunci gajiyar shirin a nan gaba kadan.
Yace shirin bada tallafin kayan noman mai taken “Tallafawa Manoman Kwara ta Tsakiya: Bude hanyoyin dogaro da kai wajen samar da abinci,” na da nufin tallafa ayyukan noma da habbaka samun yabanya ga manoman mazabar.
“Tasirin sauyin yanayi da kuma yawaitar noman gonaki yana da illa ga ingancin kasar noma. Wannan ya haifar da raguwar amfanin amfanin gonar da ake samu.
“Yana da mahimmanci in jaddada cewa ni da kaina na sayi buhunan taki guda 3,500 da aka raba a yau domin karfafa wa manomanmu gwiwa da inganta amfanin gonakinsu,” in ji Sanata Mustafa.
Mustapha ya bayyana cewa rabon taki mai yawa irin wannan na nuni da yadda ake zuba jari mai yawa a fannin noma, wanda hakan ke nuna aniyar inganta samar da abinci da tallafawa rayuwar manoma domin bunkasa noman abinci a jihar.
Sanatan na Kwara ya yi amfani da wannan dama wajen nuna wasu daga cikin nasarorin da ya samu cikin shekara daya da shafe a matsayinsa na dan majalisa da ya hada da gudanar da aikin sake gina titi Mai tsawon kilomita daya a daura da Jami’ar Al-Hikmah wanda ya dangana da titin Oke zuwa Foma a karamar hukumar Ilorin ta yamma.
Ya kara da cewa, an kuma gina rijiyoyin burtsatse masu amfani da hasken rana da sanya fitulun titi a fadin kananan hukumomin hudu na mazabar domin taimakawa kokarin gwamnatin jihar na ganin jama’a sun samu tsaftataccen ruwan sha.
REL : TSIBIRI
-
Labarai3 days agoIran ta Tabbatar da Kisan Ayatollah Khamenei a Hare-haren Amurka da Isra’ila
-
Labarai4 days agoMajalisar Dokokin Jihar Kaduna Ta Amince da Kasafin Kudin Kananan Hukumomin Jihar na 2026
-
Labarai4 days agoAzumin Ramadan: Shugaban Karamar Hukumar Birnin Kudu Ya Bada Tallafin Kudi ga Marasa Galihu
-
Labarai7 days agoUwargidan Gwamnan Zamfara Ta Kaddamar da Rabon Tallafin Ramadan ga Marasa Galihu
-
Labarai6 days agoWani Bam Kirar Hannu Ya Fashe a Kan Hanyar Gusau Zuwa Funtua
-
Labarai4 days agoBankin Raya Kasashen Afirka Zai Samar da Shirin Bunƙasa Aikin Noma a Jigawa
-
Labarai1 day agoGwamna Namadi Ya Raba Tallafin Ramadan ga Ma’aikata da Marasa Galihu
-
Labarai4 days agoMasarautar Hadejia ta Raba Zakkar Kayan Amfanin Gona da Dabbobi a Garin Unik
