Labarai
Jirgin Farko Na Alhazan Jihar Jigawa Zai Tashi A Yau Litinin
Hukumar jin dadin alhazai ta jihar Jigawa ta ce za a fara jigilar maniyyata na bana daga ranar Litinin 3 ga watan Yuni 2024.
Babban Daraktan hukumar Alhaji Ahmed Umar Labbo ya bayyana haka ga wakilinmu Usman Mohammed Zaria a Dutse.
Ya bayyana cewa Alhazan za su tashi ne daga filin jirgin Nuhu Muhammadu Sunusi zuwa kasar Saudiyya a cikin jirgin Max Air.
Alhaji Ahmed Umar Labbo ya yi nuni da cewa hukumar ta kammala shirye-shiryen jigilar Alhazai zuwa kasa mai tsarki, inda a halin yanzu an samar da takardun izinin shiga kasar ta Saudiyya wato biza ga Alhazan jihar.
Ya kuma bukaci Alhazai da su rika karbar umarni daga jami’an shiyyarsu na kananan hukumomi.
Ya bayyana cewa hukumar ta tsara dabarun tabbatar da tsaron Alhazanta a yayin da suke sansanin Alhazai da ke fanisau.
Alhaji Ahmed Umar Labbo ya kuma gargadi maniyyatan da su guji daukar abubuwan da aka haramta a cikin jakunkunansu.
Ya yi nuni da cewa, wajibi ne Alhazan su guji daukar abubuwa da suka hada da wukake da almakashi da makamantansu a jakunkunansu.
Babban Daraktan ya ce hukumar ta kuma gargadi Alhazan jihar kan daukar turare a cikin gwangwani, musamman dan feshi.
Usman Muhammad Zaria
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
-
Labarai6 days agoMasu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki
