Labarai
Karamar Hukumar Kiyawa Ta Raba Harami Da Kudade Ga Mahajjata
Majalisar karamar hukumar Kiyawa ta bada gudunmawar naira dubu dari bakwai ga maniyyatan aikin hajjin bana na yankin.
Shugaban karamar hukumar, Alhaji Nasiru Ahmad ya bayyana haka lokacin da yake jawabin ban kwana ga maniyyatan a sakatariyar karamar hukumar.
Ya ce kowane maniyyaci zai karbi naira dubu ashirin, haka kuma maniyyata maza za su karbi Harami, yayin da aka rabawa maniyyata mata turamen atamfa.
A don haka, ya bukaci maniyyatan yankin su zama jakadu nagari a lokacin da suke kasa mai tsarki.
A jawabansu daban daban jami’in shiyya na hukumar jin dadin alhazai, Abdullahi Abubakar Garba da mataimakin daraktan ma’aikata na karamar hukumar Kiyawa, Alhaji Rabiu Tela sun yabawa shugaban karamar hukumar bisa wannan tallafi da ya baiwa maniyyatan.
A jawabin ta na godiya a madadin maniyyata mata, Malama Maimuna Muhammad ta bada tabbacin maniyyatan za su ci gaba da yin addu’o’in neman dorewar zaman lafiya da karuwar arziki ga karamar hukumar Kiyawa da jihar Jigawa da ma kasa baki daya.
Usman Mohammed Zaria
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
-
Labarai6 days agoMasu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki
