Connect with us

Labarai

Wasu masu neman dama ne suka ƙwace zanga-zangarmu – Matasan Nepal

Published

on

Matasan Nepal da suka gudanar da zanga-zangar cin hanci da rashawa sun yi iƙirarin cewa wasu masu neman dama ne suka ƙwace zanga-zangar, suka rikiɗe ta zuwa tashin hankali da ɓarna yayin da sojojin Nepal suka fito sintiri a titunan Kathmandu, inda ƙasar mai tsaunuka ke fama da tashin hankali mafi muni cikin shekaru da dama.

Zanga-zangar da aka fara da nufin adawa da cin hanci da son kai ta rikiɗe a ranar Talata zuwa ƙone-kone da tashin hankali.

Firaministan ƙasar dai ya yi murabus bayan gidajen ’yan siyasa sun shiga hannun masu zanga-zangar tare da banka wa gine-ginen gwamnati wuta, har ma aka kutsa majalisar dokoki aka cinna mata wuta.

Ƙungiyoyin matasa sun nesanta kansu daga ɓarnar, suna masu cewa masu son yin amfani da dama ne suka shiga suka lalata zanga-zangar.

Sojoji sun kafa dokar hana fita a faɗin ƙasa har zuwa safiyar Alhamis, suna gargadin hukunta duk wanda aka samu da hannu a tashin hankali ko barna.

Rahotanni sun ce an kama mutum 27 da ake zargi da hannu a fashi da tarzoma, tare da ƙwato bindigogi 31.

Sojojin sun ce suna ƙoƙarin shawo kan lamarin da ke ƙara dagulewa, musamman bayan murabus ɗin Firaminista KP Sharma Oli ya haifar da giɓin shugabanci.

Labarai

Labarai4 hours ago

Hukumar Kula da Kogin Benuwe ta Dauki Matakin Yashe Laka da Yashi da ke Barazana ga Noman Rani

Ayyukan ban ruwa a yankin Kogin Benuwe na fuskantar barazana sakamakon taruwar Laka da Yashi a kogin, lamarin da ke...

Labarai1 day ago

Gwamna Namadi Ya Raba Tallafin Ramadan ga Ma’aikata da Marasa Galihu

Daga Usman Muhammad Zaria Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya raba tallafin kayan abinci na watan Ramadan tare da...

Labarai1 day ago

Sojoji Sun Yi Nasarar Kwato Dabbobi 257 da Aka Sace a Karamar Hukumar Gwarzo

Daga Abdullahi Jalaluddeen Sojojin Najeriya sun sami nasarar dawo da Shanu da Awaki  257 da aka sata a  wani aikin...

Labarai1 day ago

Uwargidan Gwamnan Zamfara ta Yaba da Yadda Aka yi Rabon Tallafin Ramadan

Daga Aminu Dalhatu  Uwargidan Gwamnan Jihar Zamfara, Hajiya Huriyya Dauda Lawal, ta yaba wa dukkan masu ruwa da tsaki bisa...

Labarai1 day ago

Gwamnatin Kebbi Za ta Raba Hatsi da Kayayyakin Aikin Gona ga Marasa Galihu

Daga Sani Dutsinma Gwamnatin Jihar Kebbi ta kammala shirye-shiryen raba kayayyakin aikin noma da nau’o’in hatsi daban-daban ga mutane miliyan...

Labarai1 day ago

Gwamnatin Kwara Ta Jaddada Kudurinta Na Kula Da Jin Daɗin Masu Harkar Sufuri

Gwamnatin Jihar Kwara ta bai wa masu harkar sufuri a jihar tabbacin ci gaba da kare muradunsu da jin daɗinsu....

Labarai1 day ago

Gwamnan Zamfara Ya Haramta Karbar Kudin Haraji A Hannu

Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya bayar da umarnin dakatar da duk wani tsarin karbar kuɗaɗen shiga ta tsabar kuɗi...

Labarai1 day ago

Gwamnatin Tarayya Ta Faɗaɗa Rijistar Tallafin Jama’a Domin Tantance Masu Buƙata

Gwamnatin Tarayya na faɗaɗa tare da ƙarfafa Rijistar Tallafin Jama’a ta Ƙasa National Social Register domin tabbatar da cewa an...

Labarai1 day ago

Gwamna Idris Ya Ba da Umarnin Binciken Gobarar da Ta Tashi a Makarantar Nurul Haqq da ke Birnin Kebbi

Gwamnan Jihar Kebbi, Nasir Idris, ya bayar da umarnin gaggauta kafa wani kwamitin bincike mai ƙarfi domin gano musabbabin gobarar...

Labarai1 day ago

Taraba Ta Kaddamar da Rarraba Kayan Aikin A Kananan Hukumomi 16

Hukumar Kula da Ci gaban Kiwon Lafiyar Matakin Farko ta Jihar Taraba ƙarƙashin Shirin IMPACT, ta ƙaddamar da rarraba kayan...

Mafi Shahara