Labarai
Shugaba Tinubu Ya Rantsar da Taiwo Oyedele Ministan Kudi
Daga Bello Wakili
Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya rantsar da Taiwo Oyedele a matsayin Minista a Ma’aikatar.
An gudanar da bikin rantsarwar a Fadar Shugaban Ƙas, inda Shugaba Tinubu ya taya sabon ministan murna, tare da bayyana kwarin gwiwarsa kan cewa zai taimaka wajen aiwatar da manufofin gyaran tattalin kasa.
Shugaban ƙasar ya yaba wa Oyedele kan rawar da ya taka wajen jagorantar kokarin gyara tsarin haraji na Najeriya, inda ya bayyana cewa tsohon tsarin harajin ƙasar ya tsufa kuma yana bukatar sabuntawa domin ya taimaka wajen bunƙasa tattalin arziki da kuma tabbatar da gaskiya da rikon amana.

A nasa jawabin, sabon Ministan ya gode wa Shugaban ƙasa bisa amincewar da ya nuna masa, yana mai cewa damar da aka ba shi ta yi wa ƙasa hidima babbar abar alfahari ce.
Ya kuma tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa zai ba da dukkan ƙoƙarinsa wajen gudanar da aikinsa, yana mai cewa manufofin kudin gwamnati za su mayar da hankali kan ƙarfafa tattara kudaden shiga, inganta yadda ake kashe kuɗi, da kuma tabbatar da dorewar tattalin arzikin ƙasa.
-
Labarai6 days agoAn Nada Kabir Yahaya Darakta Janar na Farko na Filin Jirgin Sama da ke Gusau
-
Labarai5 days agoTinubu Ya Nada Lamido Yuguda Mataimakin Gwamnan Babban Bankin Kasa
-
Labarai6 days agoKwastam ta Kama Kayayyaki na Sama da Naira Miliyan 478 a Jihar Kwara
-
Labarai4 days agoJami’ar Bayero Kano Ta Yi Martani Kan Zargin Damfarar Dalibi
-
Labarai4 days agoKwastam Ta Kama Kayayyakin Fasa Kwauri Na Naira Miliyan 478 A Kwara
-
Labarai4 days agoAn Yi Wa Jami’an FRSC A Jos Gwajin Idanu Kyauta Domin Ranar Glaucoma Ta Duniya
-
Labarai4 days agoMatashi Mai Digiri Na Farko Na Sayar Da Ruwan Leda A Taraba
-
Labarai1 day agoJIBWIS Ta Bukaci Gwamna Bago Ya Gaggauta Sanya Hannu Kan Dokar Hisbah
