Connect with us

Kasuwanci

Ranar Mata: UNICEF Da Jihar Jigawa Sun Horar Sa Mata 600 Shirin Jari Bola

Published

on

Asusun kula da kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya (UNICEF) tare da hadin gwiwar gwamnatin jihar Jigawa, sun fara horas da mata 600 kan inganta muhalli ta hanyar bola jari.

Shugaban Hukumar Kare Muhalli ta Jihar Jigawa JISEPA, Alhaji Adamu Sabo ya bayyana haka a wajen taron tunawa da ranar mata ta duniya da kuma fara horaswar da aka gudanar a Dutse.

Alhaji Adamu Sabo ya ce, baya ga  jajircewa, da juriya, da nasarorin da mata suke da, bikin ya yi duba kan irin rawar da mata suke takawa wajen dorewar muhalli da bunkasar tattalin arziki.

Ya jaddada cewa ta hanyar shirin bola jari, watiWaste to Wealth Initiative, za su iya baiwa mata damar kare muhalli da kuma samar da kyakkyawan yanayi ga iyalansu.

Shugaban hukumar ya bayyana cewa, duk da kalubalen da ake fuskanta a duniya a fannin sarrafa shara, da kuma yadda ake zubar da shara ba bisa ka’ida ba,  da ke barazana ga muhalli, har yanzu akwai damar da za a iya maida sharar da aka tara a gida zuwa dukiya.

Ya ce horon zai koyar da mata yadda za su yi kasuwanci da sharar da suka tara a gida, tare da tabbatar da karfafa tattalin arziki da kuma inganta muhalli.

Ya kara da cewa, hakan zai baiwa mata matasa damar ba da gudumawa wajen samun kudaden shiga a gida da kuma ci gaban tattalin arzikin kasa.

Bugu da ƙari, shugaban na JISEPA  ya bayyana cewa horaswar za ta yi amfani da shirin da UNICEF ta fara na “Samun Damarar Kasuwanci ga Matasa” (YOMA), wani sabon tsarin na dandali ta yanar gizo, da ke haɗa matasa daga ko’ina a fadin duniya  don koyon kasuwanci,  da samun kuɗi, da tasirin zamantakewa.

Adamu Sabo ya yabawa masu ruwa da tsaki da suka goyi bayan wannan shiri da suka hada da kungiyar jari bola  ta Najeriya WAPAN, da gwamnan jihar Jigawa Malam Umar Namadi bisa goyon bayan da suka bayar.

A jawabinta lokacin da take bayyana bude horaswar, uwargidan gwamnan jihar Jigawa, Hajiya Amina Umar Namadi, ta yaba da kokarin hukumar da sauran masu ruwa da tsaki da suka taimata wajan samun nasarar horon.

Ta ce shigar da mata cikin shirin inganta  muhalli ba shakka zai samar da wani tasiri, ba a Jigawa kadai ba har ma a duniya baki daya.

Ta yi kira ga mahalarta taron da su yi amfani da damar da suka samu wajen inganta rayuwarsu, baya ga ba da gudummawa wajen tsaftace muhallinsu.

Taken ranar Mata ta Duniya ta 2025 shi ne, “Bayar Da Dama ga Mata da ‘Yan Mata: Hakkoki, Daidaito, da  Ƙarfafawa, “wanda ke kira ga bai wa mata hakkokinsu, da samar musu da damarmaki,  ba tare da an bar su a baya ba.”

Usman Muhammad Zaria

Labarai

Labarai9 hours ago

Hukumar Kula da Kogin Benuwe ta Dauki Matakin Yashe Laka da Yashi da ke Barazana ga Noman Rani

Ayyukan ban ruwa a yankin Kogin Benuwe na fuskantar barazana sakamakon taruwar Laka da Yashi a kogin, lamarin da ke...

Labarai1 day ago

Gwamna Namadi Ya Raba Tallafin Ramadan ga Ma’aikata da Marasa Galihu

Daga Usman Muhammad Zaria Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya raba tallafin kayan abinci na watan Ramadan tare da...

Labarai1 day ago

Sojoji Sun Yi Nasarar Kwato Dabbobi 257 da Aka Sace a Karamar Hukumar Gwarzo

Daga Abdullahi Jalaluddeen Sojojin Najeriya sun sami nasarar dawo da Shanu da Awaki  257 da aka sata a  wani aikin...

Labarai1 day ago

Uwargidan Gwamnan Zamfara ta Yaba da Yadda Aka yi Rabon Tallafin Ramadan

Daga Aminu Dalhatu  Uwargidan Gwamnan Jihar Zamfara, Hajiya Huriyya Dauda Lawal, ta yaba wa dukkan masu ruwa da tsaki bisa...

Labarai1 day ago

Gwamnatin Kebbi Za ta Raba Hatsi da Kayayyakin Aikin Gona ga Marasa Galihu

Daga Sani Dutsinma Gwamnatin Jihar Kebbi ta kammala shirye-shiryen raba kayayyakin aikin noma da nau’o’in hatsi daban-daban ga mutane miliyan...

Labarai2 days ago

Gwamnatin Kwara Ta Jaddada Kudurinta Na Kula Da Jin Daɗin Masu Harkar Sufuri

Gwamnatin Jihar Kwara ta bai wa masu harkar sufuri a jihar tabbacin ci gaba da kare muradunsu da jin daɗinsu....

Labarai2 days ago

Gwamnan Zamfara Ya Haramta Karbar Kudin Haraji A Hannu

Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya bayar da umarnin dakatar da duk wani tsarin karbar kuɗaɗen shiga ta tsabar kuɗi...

Labarai2 days ago

Gwamnatin Tarayya Ta Faɗaɗa Rijistar Tallafin Jama’a Domin Tantance Masu Buƙata

Gwamnatin Tarayya na faɗaɗa tare da ƙarfafa Rijistar Tallafin Jama’a ta Ƙasa National Social Register domin tabbatar da cewa an...

Labarai2 days ago

Gwamna Idris Ya Ba da Umarnin Binciken Gobarar da Ta Tashi a Makarantar Nurul Haqq da ke Birnin Kebbi

Gwamnan Jihar Kebbi, Nasir Idris, ya bayar da umarnin gaggauta kafa wani kwamitin bincike mai ƙarfi domin gano musabbabin gobarar...

Labarai2 days ago

Taraba Ta Kaddamar da Rarraba Kayan Aikin A Kananan Hukumomi 16

Hukumar Kula da Ci gaban Kiwon Lafiyar Matakin Farko ta Jihar Taraba ƙarƙashin Shirin IMPACT, ta ƙaddamar da rarraba kayan...

Mafi Shahara