Labarai
NSCDC Ta Tura Jami’ai Sama da 2000 Kananan Hukumomin Jihar Kaduna Gabanin Bukukuwan Kirsimeti
Daga Usman Sani
Kwamandan Hukumar Tsaron Farin Kaya ta Civil Defence (NSCDC) a Jihar Kaduna, Panam Musa Buba, ya bayar da umarnin tura jami’an tsaro a dukkan kananan hukumomi ashirin da uku na jihar.
A wannan karo, ya umurci a tura jami’ai dubu biyu da ɗari (2,100) domin tabbatar da tsaron al’umma a lokacin bukukuwan ƙarshen shekara.
Wata sanarwa da Jami’in Hulɗa da Jama’a na rundunar jihar, SC Habeeb Badamasi, ya fitar, ta bayyana cewa an daukin matakin hakan ne da nufin ƙarfafa tsaro kafin Kirsimeti, da lokacin Kirsimetin da bayan bukukuwan Kirsimeti da Sabuwar Shekara.
Kwamandan Panam Musa Buba ya tabbatar wa mazauna jihar cewa za su ci gaba da harkokinsu na yau da kullum cikin kwanciyar hankali, inda ya jaddada ƙudurin rundunar wajen kare rayuka da dukiyoyin al’umma a tsawon lokacin bukukuwan.
“Mun zo ne domin tabbatar da zaman lafiya da tsaro, domin kowa ya more wannan lokaci na bukukuwa cikin natsuwa,” In ji shi.
Haka kuma, ya gargaɗi masu aikata laifuka da su janye daga duk wani shiri na aikata laifi, yana mai bayyana cewa jami’an NSCDC tare da sauran hukumomin tsaro za su kasance a wurare masu muhimmanci domin hana aikata laifuka.
“Jami’anmu sun shirya tsaf, a don haka, duk wanda ya zabi aikata laifi zai fuskanci hukunci mai tsauri,” in ji Kwamandan.
Kwamandan Panam Buba ya kuma bukaci al’ummar Kirista da su yi amfani da wannan lokaci na bukukuwa wajen tunani da nazari kan ainihin ma’anar Kirsimeti.
-
Labarai2 days agoIran ta Tabbatar da Kisan Ayatollah Khamenei a Hare-haren Amurka da Isra’ila
-
Labarai4 days agoMajalisar Dokokin Jihar Kaduna Ta Amince da Kasafin Kudin Kananan Hukumomin Jihar na 2026
-
Labarai4 days agoAzumin Ramadan: Shugaban Karamar Hukumar Birnin Kudu Ya Bada Tallafin Kudi ga Marasa Galihu
-
Labarai6 days agoUwargidan Gwamnan Zamfara Ta Kaddamar da Rabon Tallafin Ramadan ga Marasa Galihu
-
Labarai6 days agoWani Bam Kirar Hannu Ya Fashe a Kan Hanyar Gusau Zuwa Funtua
-
Labarai3 days agoBankin Raya Kasashen Afirka Zai Samar da Shirin Bunƙasa Aikin Noma a Jigawa
-
Labarai3 days agoGwamnatin Jigawa ta Gargadi ‘Yan Kwangila Kan Ingancin Abincin Ramadan
-
Labarai3 days agoMasarautar Hadejia ta Raba Zakkar Kayan Amfanin Gona da Dabbobi a Garin Unik
