Labarai
NIPR Ta Bai Wa Gwamnan Jigawa Lambar Yabo Ta Musamman Bisa Samar Da Abinci Ga Kasa
Gwamna Umar Namadi na jihar Jigawa ya yi alkawarin aiwatar da wasu tsare-tsare da za su bunkasa noma da sauran abubuwan da suka shafi bunkasa noma a jihar.

Ya bayyana haka ne a Dutse a wani gagarumin biki da Cibiyar Koyar da Dabarun Yada Labarai da Hulda da Jama’a ta Kasa NIPR ta shirya, inda ta ba shi lambar yabo ta musamman a fannin samar da abinci.

Gwamna Umar Namadi ya bayyana cewa daya daga cikin dabarun ci gaban gwamnatin jihar shi ne tabbatar da dorewar aikin noma da nufin samar da ayyukan yi a jihar.

Gwamna Namadi ya yi nuni da cewa, fifikon da gwamnatin jihar ta bai wa noma shi ya sa jihar ta kasance kan gaba wajen samar da wasu kayan abinci da kudi a kasar nan da suka hada da alkama, shinkafa, ridi da ganyen zobarodo.

Ya ce, wannan kokarin ya kuma sanya jihar ta zamto kan gaba a fannin bayar da gudunmawa wajen samar da abinci ga kasa da habbaka tattalin arzikin kasa.

Ya bayyana cewa bunkasa fannin noma ya yi daidai da burin ci gaba mai dorewa na kawo karshen yunwa, da samar da wadataccen abinci da inganta abinci mai gina jiki da kuma bunkasa noma mai dorewa.

Namadi ya godewa NIPR bisa wannan karramawar sannan ya yi alkawarin bullo da wasu tsare-tsare da za su kawo sauyi a fannin noma a jihar.

Tun da farko a nasa jawabin, shugaban NIPR Dakta Ike Neliaku, ya ce lambar yabo ta NIPR na da nufin karfafa kyakkyawan shugabanci a matakai daban-daban na gwamnati.
Ya kuma yabawa gwamnan kan wasu tsare-tsare da suka karfafa samar da abinci wanda kuma ya samar da ayyukan yi ga dubban jama’a tare da bunkasa darajar aikin gona.

A halin da ake ciki, kwamishinan yada labarai, da kwamishinan Kudi, da na kananan hukumomi na jihar Jigawa sun yi jawabai daban daban kan tasirin aikin sauya fasalin noma na jihar Jigawa ga harkokin tsaro da sauran bangarori daban daban na jihar.
Gidan Rediyon Najeriya ya ruwaito cewa, an bai wa Gwamna Umar Namadi matsayin Uban cibiyar ta NIPR reshen jihar Jigawa.
Usman Muhammad Zaria
-
Labarai3 days agoIran ta Tabbatar da Kisan Ayatollah Khamenei a Hare-haren Amurka da Isra’ila
-
Labarai4 days agoMajalisar Dokokin Jihar Kaduna Ta Amince da Kasafin Kudin Kananan Hukumomin Jihar na 2026
-
Labarai4 days agoAzumin Ramadan: Shugaban Karamar Hukumar Birnin Kudu Ya Bada Tallafin Kudi ga Marasa Galihu
-
Labarai7 days agoUwargidan Gwamnan Zamfara Ta Kaddamar da Rabon Tallafin Ramadan ga Marasa Galihu
-
Labarai4 days agoBankin Raya Kasashen Afirka Zai Samar da Shirin Bunƙasa Aikin Noma a Jigawa
-
Labarai6 days agoWani Bam Kirar Hannu Ya Fashe a Kan Hanyar Gusau Zuwa Funtua
-
Labarai1 day agoGwamna Namadi Ya Raba Tallafin Ramadan ga Ma’aikata da Marasa Galihu
-
Labarai3 days agoGwamnatin Jigawa ta Gargadi ‘Yan Kwangila Kan Ingancin Abincin Ramadan
