Connect with us

Labarai

Muna Samun Gagarumin Cigaba Wajen Dawo Da Zaman Lafiya A Zamfara-Gwamna Lawal

Published

on

Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya jaddada cewa yaki da matsalar rashin tsaro a jihar nauyi ne na  gwamnatinsa da sauran masu ruwa da tsaki, da ma al’umma baki.

Wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Sulaiman Bala Idris, ya fitar a ranar Litinin, ta ce gwamnan ya bayyana hakan ne yayin da yake jagorantar taron majalisar zartarwa ta jihar karo na 18 da aka gudanar a fadar gwamnati da ke Gusau.

Sanarwar ta ce, majalisar ta tattauna kan muhimman batutuwa da suka shafi jihar, ciki har da tsaro, ilimi, kiwon lafiya, da cigaban ayyukan raya kasa.

Dr. Lawal ya tunatar da mambobin majalisar muhimmancin hadin kan su wajen yaki da rashin tsaro a karkashin wannan gwamnati.

Muna samun gagarumin ci gaba wajen dawo da zaman lafiya a mafi yawan sassan jihar. An raunana karfin ‘yan bindiga fiye da yadda ake gani a baya,” in ji shi.

Ya bukaci mambobin majalisar su kasance masu saurin daukar mataki, tare da kusanci da al’ummarsu da zababbun shugabannin kananan hukumomi, da kuma ci gaba da bayar da rahoton halin tsaro ga Kwamishinan Tsaro na Jihar.

Haka kuma, mu ci gaba da addu’a domin shahidanmu da suka rasa rayukansu wajen kare jama’a,” in ji gwamnan.

Gwamna Lawal ya kuma shawarci mambobin majalisar da su ci gaba da kyakkyawar dangantaka da sauran jami’an gwamnati da zababbun wakilai domin tabbatar da ingantacciyar gwamnati da samar da ayyuka ga jama’a.

 

AMINU DALHATU

Labarai

Labarai3 hours ago

Hukumar Kula da Kogin Benuwe ta Dauki Matakin Yashe Laka da Yashi da ke Barazana ga Noman Rani

Ayyukan ban ruwa a yankin Kogin Benuwe na fuskantar barazana sakamakon taruwar Laka da Yashi a kogin, lamarin da ke...

Labarai23 hours ago

Gwamna Namadi Ya Raba Tallafin Ramadan ga Ma’aikata da Marasa Galihu

Daga Usman Muhammad Zaria Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya raba tallafin kayan abinci na watan Ramadan tare da...

Labarai1 day ago

Sojoji Sun Yi Nasarar Kwato Dabbobi 257 da Aka Sace a Karamar Hukumar Gwarzo

Daga Abdullahi Jalaluddeen Sojojin Najeriya sun sami nasarar dawo da Shanu da Awaki  257 da aka sata a  wani aikin...

Labarai1 day ago

Uwargidan Gwamnan Zamfara ta Yaba da Yadda Aka yi Rabon Tallafin Ramadan

Daga Aminu Dalhatu  Uwargidan Gwamnan Jihar Zamfara, Hajiya Huriyya Dauda Lawal, ta yaba wa dukkan masu ruwa da tsaki bisa...

Labarai1 day ago

Gwamnatin Kebbi Za ta Raba Hatsi da Kayayyakin Aikin Gona ga Marasa Galihu

Daga Sani Dutsinma Gwamnatin Jihar Kebbi ta kammala shirye-shiryen raba kayayyakin aikin noma da nau’o’in hatsi daban-daban ga mutane miliyan...

Labarai1 day ago

Gwamnatin Kwara Ta Jaddada Kudurinta Na Kula Da Jin Daɗin Masu Harkar Sufuri

Gwamnatin Jihar Kwara ta bai wa masu harkar sufuri a jihar tabbacin ci gaba da kare muradunsu da jin daɗinsu....

Labarai1 day ago

Gwamnan Zamfara Ya Haramta Karbar Kudin Haraji A Hannu

Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya bayar da umarnin dakatar da duk wani tsarin karbar kuɗaɗen shiga ta tsabar kuɗi...

Labarai1 day ago

Gwamnatin Tarayya Ta Faɗaɗa Rijistar Tallafin Jama’a Domin Tantance Masu Buƙata

Gwamnatin Tarayya na faɗaɗa tare da ƙarfafa Rijistar Tallafin Jama’a ta Ƙasa National Social Register domin tabbatar da cewa an...

Labarai1 day ago

Gwamna Idris Ya Ba da Umarnin Binciken Gobarar da Ta Tashi a Makarantar Nurul Haqq da ke Birnin Kebbi

Gwamnan Jihar Kebbi, Nasir Idris, ya bayar da umarnin gaggauta kafa wani kwamitin bincike mai ƙarfi domin gano musabbabin gobarar...

Labarai1 day ago

Taraba Ta Kaddamar da Rarraba Kayan Aikin A Kananan Hukumomi 16

Hukumar Kula da Ci gaban Kiwon Lafiyar Matakin Farko ta Jihar Taraba ƙarƙashin Shirin IMPACT, ta ƙaddamar da rarraba kayan...

Mafi Shahara