Kasuwanci
Maniyatan Jigawa 550 Sun Isa Kasa Mai Tsaki Don Aikin Hajjin Bana
An dauke kashin farko na maniyyata 550 daga jihar jigawa zuwa Saudiyya a filin jirgin Nuhu Muhammadu Sunusi domin gudanar da aikin hajjin shekarar 2025.
Babban Daraktan hukumar Alhaji Ahmed Umar Labbo ya bayyana hakan jim kadan bayan tashinsu zuwa kasa mai tsarki.
Ya bayyana cewa maniyyatan sun fito ne daga kananan hukumomi 24 na jihar.
Ya ce kananan hukumomin sun hada da Kazaure, Roni, Gwiwa, Yankwashi, Gumel, Gagarawa, Garki, Maigatari, Suletankarkar, Babura, Jahun, da Miga.
Sauran sune Kafin Hausa, Auyo, Hadejia, Kirikasamma, Guri, Birniwa, Malam Madori, Dutse, Kiyawa, Ringim da Gwaram.
Alhaji Ahmed Umar Labbo, ya yi nuni da cewa jirgin ya kuma kunshi wasu jami’an hukumar alhazai ta jiha da na likitoci da sauran masu ruwa da tsaki.
Ya bukace su da su kasance jakadu nagari na jiha da kasa baki daya yayin da suke kasa mai tsarki.
Labbo, ya yabawa jami’an tsaron jihar bisa yadda suka gudanar da aikin tantancewar a sansanin Hajji da filin jirgin sama.
Ya kuma yabawa gwamnan jihar Malam Umar Namadi bisa goyon baya da hadin kai da ake baiwa hukumar a kowane lokaci.
Shima da yake jawabi, Daraktan ayyuka na hukumar Alhaji Arab Sabo Aujara ya yi nuni da cewa, jihar ta yi wa maniyyata karfin gwiwa ta hanyar gayyato hukumomin gwamnatin tarayya da suka hada da hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA da shige da fice da kuma kwastam domin fadakar da mahajjatan abubuwan da za a dauka tare da sauran abubuwan da aka haramta.
Ya bukace su da su ji tsoron Allah a cikin ayyukansu yayin da suke kasa mai tsarki.
Arab ya kara da cewa, jihar ta tanadi komai don tabbatar da jin dadi da walwala a kasar ta Saudiyya
Wasu daga cikin mahajjatan da suka zanta da gidan rediyon Najeriya kafin tashin su, sun yabawa gwamnatin jihar da hukumar alhazai bisa yadda suka yi musu jinya a sansanin alhazai da filin jirgin sama.
Wakilinmu ya ruwaito cewa, kamfanin jirgin Max Air ne ya dauke alhazan.
USMAN MZ
-
Labarai3 days agoIran ta Tabbatar da Kisan Ayatollah Khamenei a Hare-haren Amurka da Isra’ila
-
Labarai4 days agoMajalisar Dokokin Jihar Kaduna Ta Amince da Kasafin Kudin Kananan Hukumomin Jihar na 2026
-
Labarai4 days agoAzumin Ramadan: Shugaban Karamar Hukumar Birnin Kudu Ya Bada Tallafin Kudi ga Marasa Galihu
-
Labarai6 days agoUwargidan Gwamnan Zamfara Ta Kaddamar da Rabon Tallafin Ramadan ga Marasa Galihu
-
Labarai6 days agoWani Bam Kirar Hannu Ya Fashe a Kan Hanyar Gusau Zuwa Funtua
-
Labarai3 days agoBankin Raya Kasashen Afirka Zai Samar da Shirin Bunƙasa Aikin Noma a Jigawa
-
Labarai3 days agoGwamnatin Jigawa ta Gargadi ‘Yan Kwangila Kan Ingancin Abincin Ramadan
-
Labarai3 days agoMasarautar Hadejia ta Raba Zakkar Kayan Amfanin Gona da Dabbobi a Garin Unik
