Labarai
Nasarorin Ma’aikatar Ayukka a Karkashin Shirin “Renewed Hope”
Gwamnatin Tarayya ta fitar da cikakken rahoto na tsakiyar zangon mulki da ke bayyana muhimman nasarorin da Ma’aikatar Ayyuka ta Tarayya ta cimma daga watan Mayu 2023 zuwa Afrilu 2025.
Rahoton, wanda Ofishin Mai Ba Shugaban Ƙasa Shawara kan Tsare-Tsare da Daidaita Ayyuka ya gabatar, ya bayyana ci gaba mai ma’ana da aka samu a fannin gine-ginen ababen more rayuwa, musamman hanyoyi, karkashin shirin Renewed Hope Action Plan na Shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Daya daga cikin manyan nasarorin da rahoton ya nuna shi ne ci gaba da aiwatar da shirin Highway Development and Management Initiative (HDMI), wanda ke amfani da tsarin haɗin gwiwa tsakanin gwamnati da masu zaman kansu (PPP). Wannan tsarin ya ba da damar janyo hannun jari daga masu zaman kansu don gyara da gina sabbin manyan hanyoyi da ke haɗa manyan birane da cibiyoyin kasuwanci a faɗin ƙasar.
Ma’aikatar Ayyuka ta kuma canja fasaha wajen gina hanyoyi daga amfani da kwalta zuwa amfani da fasahar siminti (concrete technology), wacce aka sani da jurewa dogon lokaci da rage buƙatar gyare-gyare akai-akai.
Wannan sabon tsarin yana tabbatar da cewa hanyoyin da ake ginawa yanzu za su dawwama, za su kasance masu aminci, kuma su fi araha a nan gaba.
Rahoton ya kuma nuna yadda Ma’aikatar Ayyuka ta ke kirkirar hanyoyin samun kuɗi na musamman don aiwatar da manyan ayyuka.
Hanyoyin sun haɗa da fita kasuwa don neman jari, fitar da takardun lamuni na gine-ginen ababen more rayuwa, da kuma ƙara faɗaɗa haɗin gwiwa da masu zaman kansu.
Wannan ya taimaka wajen ɗora ma’aikatar kan tafarkin da zai kai ga ingantaccen sauyi duk da ƙalubalen tattalin arziki.
“Manufar Renewed Hope ba ƙalmar kamfen ba ce kawai — tsari ne mai rai da ake aiwatarwa a kowane yanki na Najeriya,” in ji rahoton. “Ma’aikatar Ayyuka na aiki ba dare ba rana don tabbatar da cewa al’umma sun ji daɗin wannan sauyi.”
Wasu daga cikin manyan ayyukan da ake aiwatarwa ko aka kammala sun haɗa da faɗaɗa titin Legas-Ibadan, aikin titin Abuja-Kano, da sauran hanyoyin haɗin jihohi da ke da mahimmanci ga ciniki, noma da haɗin kai na ƙasa.
Masana sun bayyana cewa waɗannan nasarori na nuni da gaskiya da nufin gyara ƙasa bisa tsari da tasiri. Da sauran shekaru biyu kafin ƙarshen wannan zangon mulki, ana sa ran za a ci gaba da jan ƙasa da sauri domin samar da ci gaba mai ɗorewa.
Ofishin Mai Ba Shugaban Ƙasa Shawara kan Tsare-Tsare da Daidaita Ayyuka (CRDCU) ya jaddada cewa bin diddigin aiki da nuna gaskiya a bainar jama’a su ne ginshiƙan tsarin mulki na Renewed Hope.
Yayin da Najeriya ke ci gaba da tafiya zuwa ga zamanancewar ababen more rayuwa, Ma’aikatar Ayyuka ta Tarayya na taka rawa mai muhimmanci wajen gina tubalin ci gaban ƙasa da haɗa al’umma da juna.
Bello Wakili
-
Labarai3 days agoIran ta Tabbatar da Kisan Ayatollah Khamenei a Hare-haren Amurka da Isra’ila
-
Labarai5 days agoMajalisar Dokokin Jihar Kaduna Ta Amince da Kasafin Kudin Kananan Hukumomin Jihar na 2026
-
Labarai5 days agoAzumin Ramadan: Shugaban Karamar Hukumar Birnin Kudu Ya Bada Tallafin Kudi ga Marasa Galihu
-
Labarai1 day agoHukumar Kula da Kogin Benuwe ta Dauki Matakin Yashe Laka da Yashi da ke Barazana ga Noman Rani
-
Labarai2 days agoGwamna Namadi Ya Raba Tallafin Ramadan ga Ma’aikata da Marasa Galihu
-
Labarai4 days agoBankin Raya Kasashen Afirka Zai Samar da Shirin Bunƙasa Aikin Noma a Jigawa
-
Labarai7 days agoWani Bam Kirar Hannu Ya Fashe a Kan Hanyar Gusau Zuwa Funtua
-
Labarai4 days agoGwamnatin Jigawa ta Gargadi ‘Yan Kwangila Kan Ingancin Abincin Ramadan
