Labarai
Kotu Ta Bada Belin Tsohon Gwamnan Jihar Kwara
Wata babbar kotun tarayya da ke Ilorin babban birnin jihar Kwara, ta bayar da belin tsohon gwamnan jihar, Alhaji Abdulfatah Ahmed a kan kudi naira miliyan hamsin, bisa zargin almubazzaranci da kudade a lokacin da yake mulki daga shekarar 2011 zuwa 2019.
Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta EFCC na tuhumar Abdulfatah bisa zargin almubazzaranci da kudaden jama’a har Naira Miliyan Dubu Daya .
Tsohon gwamnan, wanda ya kai kansa zuwa ofishin hukumar EFCC shiyyar Ilorin a ranar Litinin 19 ga watan Fabrairun 2024, an tsare shi ne bisa wasu sharuddan beli.
A hukuncin da ta yanke bayan sauraron bangarorin biyu, Mai shari’a Evelyn Anyadike ta bayar da sharuddan beli guda takwas domin sakin tsohon gwamnan.
Mai shari’a Anyadike ta ce sharuddan belin sun hada da Naira miliyan 50 , da mutum biyu da za su tsaya masa da kadarorinsu a garin Ilorin da kuma mika fasfo dinsa na tafiye-tafiye zuwa kasashen waje ga magatakardar kotun, da dai sauransu.
Da yake amsa tambayoyi daga manema labarai, lauyan hukumar EFCC Rotimi Jacobs (SAN) wanda ya bayyana cewa wanda ake kara yana kan shari’a da tuhume-tuhume 12, ya kuma ki amsa laifinsa a lokacin da aka karanta masa tuhume-tuhumen.
A nasa tsokacin, lauyan wanda ake kara, Kehinde Eleja (SAN), ya koka da yadda ake musgunawa wanda yake karewa.
An dage ci gaba da sauraron karar zuwa ranakun 29 da 30 ga watan Afrilu na wannan shekara ci gaba da domin sauraren karar
Ali Muhammad Rabi’u
-
Labarai2 days agoIran ta Tabbatar da Kisan Ayatollah Khamenei a Hare-haren Amurka da Isra’ila
-
Labarai4 days agoMajalisar Dokokin Jihar Kaduna Ta Amince da Kasafin Kudin Kananan Hukumomin Jihar na 2026
-
Labarai4 days agoAzumin Ramadan: Shugaban Karamar Hukumar Birnin Kudu Ya Bada Tallafin Kudi ga Marasa Galihu
-
Labarai6 days agoUwargidan Gwamnan Zamfara Ta Kaddamar da Rabon Tallafin Ramadan ga Marasa Galihu
-
Labarai6 days agoWani Bam Kirar Hannu Ya Fashe a Kan Hanyar Gusau Zuwa Funtua
-
Labarai3 days agoBankin Raya Kasashen Afirka Zai Samar da Shirin Bunƙasa Aikin Noma a Jigawa
-
Labarai3 days agoGwamnatin Jigawa ta Gargadi ‘Yan Kwangila Kan Ingancin Abincin Ramadan
-
Labarai3 days agoMasarautar Hadejia ta Raba Zakkar Kayan Amfanin Gona da Dabbobi a Garin Unik
