Labarai
Jihar Kwara Za Ta Rufe Karbar Kudin Aikin Hajji Ranar Juma’a
Hukumar Kula da Jin DDaɗin Alhazai ta Jihar Kwara ta ayyana ranar Juma’a 11 ga Afirilun 2025 a matsayin ranar ƙarshe da za a kammala biyan kuɗin aikin hajjin bana ga dukkan maniyyatan jihar.
Shugaban hukumar, Alhaji Abdulkadir Abdulsalam ne ya bayyana hakan a yayin wata hira da manema labarai a Ilori.
Alhaji Abdulkadir ya bayyana cewa jimillar kuɗin aikin hajjin bana ya kai naira miliyan 8,459,000.
Ya yi kira ga dukkan maniyyatan da suka fara biyan kuɗi da su tabbatar sun kammala ragowar kuɗin kafin ranar ƙarshe, wato 11 ga Afrilu, domin ba za a ƙara lokaci ba.
Alhaji Abdulsalam ya kuma buƙaci maniyyatan da su gaggauta miƙa fasfo ɗin su na tafiya ƙasashen waje ga jami’ansu domin fara aikin biza ba tare da wani jinkiri ba, yana mai jaddada cewa fasfo mai inganci da ke da aƙalla watanni shida da fara amfani ne kawai za a amince da shi.
Ya bayyana cewa miƙa fasfo da wuri na da matuƙar muhimmanci domin kauce wa jinkiri ko rikice-rikicen da ka iya tasowa wajen fitar da biza a ƙarshe.
Alhaji Abdulsalam ya shawarci maniyyatan da su kasance masu ɗabi’a tagari da yayin zamansu a kasa mai tsarki.
Ya bayyana cewa kamfanin jirgin sama na Max Air ne aka bai wa alhakin jigilar mahajjatan Jihar Kwara na shekarar 2025 hukumance, yana mai cewa hukumar alhazan na aiki kafada da kafada da kamfanin don tabbatar da tafiyar da aikin jigilar cikin kwanciyar hankali kuma akan lokaci.
Ali Muhammad Rabi’u
-
Labarai3 days agoIran ta Tabbatar da Kisan Ayatollah Khamenei a Hare-haren Amurka da Isra’ila
-
Labarai4 days agoMajalisar Dokokin Jihar Kaduna Ta Amince da Kasafin Kudin Kananan Hukumomin Jihar na 2026
-
Labarai5 days agoAzumin Ramadan: Shugaban Karamar Hukumar Birnin Kudu Ya Bada Tallafin Kudi ga Marasa Galihu
-
Labarai7 days agoUwargidan Gwamnan Zamfara Ta Kaddamar da Rabon Tallafin Ramadan ga Marasa Galihu
-
Labarai4 days agoBankin Raya Kasashen Afirka Zai Samar da Shirin Bunƙasa Aikin Noma a Jigawa
-
Labarai7 days agoWani Bam Kirar Hannu Ya Fashe a Kan Hanyar Gusau Zuwa Funtua
-
Labarai18 hours agoHukumar Kula da Kogin Benuwe ta Dauki Matakin Yashe Laka da Yashi da ke Barazana ga Noman Rani
-
Labarai2 days agoGwamna Namadi Ya Raba Tallafin Ramadan ga Ma’aikata da Marasa Galihu
