Labarai
Gwamnan Zamfara Ya Sanya Hannu Kan Dokar Kasafin 2026
Daga Aminu Dalhatu
Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya sanya hannu kan dokar Kasafin Kuɗin Shekarar 2026, bayan Majalisar Dokokin Jihar Zamfara ta amince da shi.
An gudanar da bikin sanya hannun ne a Fadar Gwamnati da ke Gusau.
Sai dai a wajen taron, gwamnan bai bayyana jimillar adadin kasafin kuɗin shekarar ta 2026 ba.
Tun a ranar 4 ga watan Disamba ne Gwamna Dauda Lawal ya gabatar da kasafin kuɗi da ya haura naira biliyan 861 na shekarar 2026 ga Majalisar Dokokin Jihar Zamfara domin amincewa.
Manyan jami’an da suka halarci taron sun haɗa da Mataimakin Gwamnan Jihar Zamfara, Mani Malam Mumini; Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Zamfara, Bilyaminu Isma’il Moriki; Sakataren Gwamnatin Jihar (SSG); Shugaban Ma’aikata (Chief of Staff); kwamishinoni da sauran manyan jami’an gwamnati.
A baya, Majalisar Dokokin Jihar Zamfara ta riga ta amince da Kudirin Kasafin Kuɗin 2026 ya zama doka, bayan gabatar da rahoton Kwamitin Majalisar kan Kuɗi da Kasafi.
Kudirin ya tanadi jimillar kasafin kuɗi na naira biliyan 871.337 domin shekarar 2026.
Yayin gabatar da rahoton kwamitin, Shugaban Kwamitin, Rilwanu Marafa Na Gambo, ya bayyana cewa dukkan Ma’aikatun Gwamnati, Hukumomi da Cibiyoyi (MDAs) a jihar sun bayyana gaban kwamitin tare da kare kasafin kuɗinsu. Ya ƙara da cewa an samu gagarumin ci gaba a tsarin samun kuɗaɗen shiga na yawancin hukumomi.
Na Gambo ya kuma bayyana cewa kwamitin ya ba da shawarar ƙara naira biliyan 8 domin ayyukan ci gaba (capital expenditure) a Ma’aikatar Kananan Hukumomi da Harkokin Sarauta, tare da ƙara naira biliyan 2 domin kuɗaɗen gudanarwa (recurrent expenditure) ga Majalisar Dokokin Jihar Zamfara.
A lokacin amincewa da kudirin, Shugaban Majalisar, Bilyaminu Isma’il Moriki, ya ce Majalisar ta yi la’akari da manyan abubuwan da ya kamata gwamnati ta fi bai wa fifiko yanzu, da suka haɗa da tsaro, noma, lafiya, ilimi da gine-gine.
Ya ce an tsara kasafin kuɗin ne domin ya dace da buƙatu da muradun al’umma a matakin ƙananan hukumomi da sauran fannoni, tare da tabbatar da daidaiton kasafi da mai da hankali sosai kan adalci da haɗa kowa da kowa.
-
Labarai2 days agoIran ta Tabbatar da Kisan Ayatollah Khamenei a Hare-haren Amurka da Isra’ila
-
Labarai4 days agoMajalisar Dokokin Jihar Kaduna Ta Amince da Kasafin Kudin Kananan Hukumomin Jihar na 2026
-
Labarai6 days agoUwargidan Gwamnan Zamfara Ta Kaddamar da Rabon Tallafin Ramadan ga Marasa Galihu
-
Labarai4 days agoAzumin Ramadan: Shugaban Karamar Hukumar Birnin Kudu Ya Bada Tallafin Kudi ga Marasa Galihu
-
Labarai6 days agoWani Bam Kirar Hannu Ya Fashe a Kan Hanyar Gusau Zuwa Funtua
-
Labarai3 days agoBankin Raya Kasashen Afirka Zai Samar da Shirin Bunƙasa Aikin Noma a Jigawa
-
Labarai3 days agoGwamnatin Jigawa ta Gargadi ‘Yan Kwangila Kan Ingancin Abincin Ramadan
-
Labarai3 days agoMasarautar Hadejia ta Raba Zakkar Kayan Amfanin Gona da Dabbobi a Garin Unik
