Connect with us

Labarai

Gwamnan Jihar Nasarawa Ya Rusa Majalisar Zartaswar Jihar

Published

on

Gwamna Abdullahi Sule na jihar Nasarawa ya rusa majalisar zartaswar jihar nan take.

Gwamnan ya kuma sallami sakataren gwamnatin jihar Barista Mohammed Uban Doma Aliyu daga mukaminsa.

Ya sanar da hakan ne yayin taron majalisar zartarwar na gaggawa da aka gudanar a gidan gwamnati da ke Lafiya, babban birnin jihar.

Ya umurci dukkan kwamishinonin da su mika al’amuran ma’aikatunsu ga manyan sakatarori, yayin da shi ma sakataren gwamnatin zai mika nasa ayyukan su ga  babban sakatare mai kula da harkokin majalisar zartaswar jihar.

Gwamna Abdullahi Sule ya yabawa ‘yan majalisar zartaswar da sakataren gwamnatin jihar, bisa yadda suka yi aiki a gwamnatinsa.

Ya kuma bayyana jajircewarsu  wajen gudanar da ayyukansu a matsayin abin yabawa, inda  ya yi fatan samun nasara a ayyukansu na gaba.

A jawabin da ya yi a madadin sauran kwamishinonin, kwamishinan shari’a kuma babban lauyan jihar Barista Labaran Shu’aibu Magaji, ya godewa gwamnan bisa damar da aka basu na yin aiki a gwamnatinsa.

 

Daga Aliyu Muraki

Labarai

Labarai15 hours ago

Hukumar Kula da Kogin Benuwe ta Dauki Matakin Yashe Laka da Yashi da ke Barazana ga Noman Rani

Ayyukan ban ruwa a yankin Kogin Benuwe na fuskantar barazana sakamakon taruwar Laka da Yashi a kogin, lamarin da ke...

Labarai1 day ago

Gwamna Namadi Ya Raba Tallafin Ramadan ga Ma’aikata da Marasa Galihu

Daga Usman Muhammad Zaria Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya raba tallafin kayan abinci na watan Ramadan tare da...

Labarai2 days ago

Sojoji Sun Yi Nasarar Kwato Dabbobi 257 da Aka Sace a Karamar Hukumar Gwarzo

Daga Abdullahi Jalaluddeen Sojojin Najeriya sun sami nasarar dawo da Shanu da Awaki  257 da aka sata a  wani aikin...

Labarai2 days ago

Uwargidan Gwamnan Zamfara ta Yaba da Yadda Aka yi Rabon Tallafin Ramadan

Daga Aminu Dalhatu  Uwargidan Gwamnan Jihar Zamfara, Hajiya Huriyya Dauda Lawal, ta yaba wa dukkan masu ruwa da tsaki bisa...

Labarai2 days ago

Gwamnatin Kebbi Za ta Raba Hatsi da Kayayyakin Aikin Gona ga Marasa Galihu

Daga Sani Dutsinma Gwamnatin Jihar Kebbi ta kammala shirye-shiryen raba kayayyakin aikin noma da nau’o’in hatsi daban-daban ga mutane miliyan...

Labarai2 days ago

Gwamnatin Kwara Ta Jaddada Kudurinta Na Kula Da Jin Daɗin Masu Harkar Sufuri

Gwamnatin Jihar Kwara ta bai wa masu harkar sufuri a jihar tabbacin ci gaba da kare muradunsu da jin daɗinsu....

Labarai2 days ago

Gwamnan Zamfara Ya Haramta Karbar Kudin Haraji A Hannu

Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya bayar da umarnin dakatar da duk wani tsarin karbar kuɗaɗen shiga ta tsabar kuɗi...

Labarai2 days ago

Gwamnatin Tarayya Ta Faɗaɗa Rijistar Tallafin Jama’a Domin Tantance Masu Buƙata

Gwamnatin Tarayya na faɗaɗa tare da ƙarfafa Rijistar Tallafin Jama’a ta Ƙasa National Social Register domin tabbatar da cewa an...

Labarai2 days ago

Gwamna Idris Ya Ba da Umarnin Binciken Gobarar da Ta Tashi a Makarantar Nurul Haqq da ke Birnin Kebbi

Gwamnan Jihar Kebbi, Nasir Idris, ya bayar da umarnin gaggauta kafa wani kwamitin bincike mai ƙarfi domin gano musabbabin gobarar...

Labarai2 days ago

Taraba Ta Kaddamar da Rarraba Kayan Aikin A Kananan Hukumomi 16

Hukumar Kula da Ci gaban Kiwon Lafiyar Matakin Farko ta Jihar Taraba ƙarƙashin Shirin IMPACT, ta ƙaddamar da rarraba kayan...

Mafi Shahara