Connect with us

Labarai

Gwamna Namadi Ya Raba Tallafin Ramadan ga Ma’aikata da Marasa Galihu

Published

on

Daga Usman Muhammad Zaria

Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya raba tallafin kayan abinci na watan Ramadan tare da bayar da tallafin kuɗi ga ma’aikatan gwamnati da na gidan gwamnati su 3,682 a jihar.

Ya bayyana cewa wannan shiri wani ɓangare ne na tsarin kula da jin daɗin ma’aikatan gwamnatinsa, wanda ke da nufin tallafa wa ma’aikata da sauran marasa ƙarfi, musamman a cikin watan Ramadan.

A cewarsa, kayan tallafin da suka haɗa da shinkafa, da taliya da sauran muhimman kayan abinci, an samar da su ne domin bai wa ma’aikata da iyalansu damar gudanar da azumi cikin sauƙi da walwala.

Ya ƙara da cewa wannan tallafi ya zo ne a matsayin kari ga sauran shirye-shiryen tallafin Ramadan da ake aiwatarwa a faɗin jihar.

Hakan ya haɗa da babban shirin ciyarwa da ake gudanarwa a kusan cibiyoyi 640 da ke cikin gundumomin siyasa 287.

Bayan samar da abinci, Gwamna Namadi ya ce shirin na kuma taimakawa tattalin arzikin cikin gida, ta hanyar samar da ayyukan wucin gadi ga kusan mutane 6,000, ciki har da masu girki da masu kula da rabon kayan abinci.

Ya kuma ƙara da cewa gwamnati ta faɗaɗa shirin domin ya haɗa da makarantun Tsangaya, inda makarantu 562 a cikin ƙananan hukumomi 27 ke cin gajiyar shirin a wannan watan Ramadan.

Da yake bayyana watan mai alfarma a matsayin lokaci na tausayi, sadaukarwa da kyautatawa, Gwamnan ya jaddada alhakin gwamnatinsa na ƙarfafa haɗin kai ta hanyar shirye-shiryen jin ƙai da aka tsara yadda ya dace.

Ya kuma ce rabon kayan abinci ga ma’aikata na nuna yadda gwamnatinsa ke girmama gudummawar da suke bayarwa wajen bunƙasa jihar. Yana mai cewa za a bai wa kowane daga cikin wadanda suka amfana da tallafin kuɗi  naira 20,000, inda jimillar kuɗin da za a raba ta haura naira miliyan 12.

Don haka, Malam Umar Namadi ya yi kira ga al’umma da su yi aiki da koyarwar addinin Musulunci ta hanyar taimakon juna tare da yin addu’o’i domin zaman lafiya, haɗin kai da ci gaba mai ɗorewa a Jihar Jigawa da Najeriya baki ɗaya.

A nasa jawabin, Kwamishinan Ma’aikatar Jin Kai, Alhaji Auwalu Sankara, ya yaba wa gwamnan bisa faɗaɗa shirye-shiryen tallafin Ramadan a jihar.

Ya ce adadin waɗanda ke amfana da shirin ciyarwar Ramadan ya ƙaru sosai a ƙarƙashin wannan gwamnati, inda ya tashi daga kusan mutane miliyan shida zuwa sama da miliyan takwas.

Ya ce ci gaba da faɗaɗa shirin a kowace shekara na nuna ƙudirin gwamnati na tabbatar da cewa babu wanda zai shiga watan Ramadan cikin yunwa.

Ma’aikatar Jin Kai da Agajin Gaggawa ce ke kula da rabon tallafin tare da haɗin gwiwar Ofishin Shugaban Ma’aikatan Jiha domin tabbatar da gaskiya da rikon amana.

Wasu daga cikin waɗanda suka amfana sun nuna godiyarsu ga Gwamna Namadi, inda suka bayyana tallafin a matsayin wanda ya zo a kan lokaci, la’akari da tsadar rayuwa da ake fuskanta a halin yanzu.

Labarai

Labarai2 hours ago

Hukumar Kula da Kogin Benuwe ta Dauki Matakin Yashe Laka da Yashi da ke Barazana ga Noman Rani

Ayyukan ban ruwa a yankin Kogin Benuwe na fuskantar barazana sakamakon taruwar Laka da Yashi a kogin, lamarin da ke...

Labarai22 hours ago

Gwamna Namadi Ya Raba Tallafin Ramadan ga Ma’aikata da Marasa Galihu

Daga Usman Muhammad Zaria Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya raba tallafin kayan abinci na watan Ramadan tare da...

Labarai1 day ago

Sojoji Sun Yi Nasarar Kwato Dabbobi 257 da Aka Sace a Karamar Hukumar Gwarzo

Daga Abdullahi Jalaluddeen Sojojin Najeriya sun sami nasarar dawo da Shanu da Awaki  257 da aka sata a  wani aikin...

Labarai1 day ago

Uwargidan Gwamnan Zamfara ta Yaba da Yadda Aka yi Rabon Tallafin Ramadan

Daga Aminu Dalhatu  Uwargidan Gwamnan Jihar Zamfara, Hajiya Huriyya Dauda Lawal, ta yaba wa dukkan masu ruwa da tsaki bisa...

Labarai1 day ago

Gwamnatin Kebbi Za ta Raba Hatsi da Kayayyakin Aikin Gona ga Marasa Galihu

Daga Sani Dutsinma Gwamnatin Jihar Kebbi ta kammala shirye-shiryen raba kayayyakin aikin noma da nau’o’in hatsi daban-daban ga mutane miliyan...

Labarai1 day ago

Gwamnatin Kwara Ta Jaddada Kudurinta Na Kula Da Jin Daɗin Masu Harkar Sufuri

Gwamnatin Jihar Kwara ta bai wa masu harkar sufuri a jihar tabbacin ci gaba da kare muradunsu da jin daɗinsu....

Labarai1 day ago

Gwamnan Zamfara Ya Haramta Karbar Kudin Haraji A Hannu

Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya bayar da umarnin dakatar da duk wani tsarin karbar kuɗaɗen shiga ta tsabar kuɗi...

Labarai1 day ago

Gwamnatin Tarayya Ta Faɗaɗa Rijistar Tallafin Jama’a Domin Tantance Masu Buƙata

Gwamnatin Tarayya na faɗaɗa tare da ƙarfafa Rijistar Tallafin Jama’a ta Ƙasa National Social Register domin tabbatar da cewa an...

Labarai1 day ago

Gwamna Idris Ya Ba da Umarnin Binciken Gobarar da Ta Tashi a Makarantar Nurul Haqq da ke Birnin Kebbi

Gwamnan Jihar Kebbi, Nasir Idris, ya bayar da umarnin gaggauta kafa wani kwamitin bincike mai ƙarfi domin gano musabbabin gobarar...

Labarai1 day ago

Taraba Ta Kaddamar da Rarraba Kayan Aikin A Kananan Hukumomi 16

Hukumar Kula da Ci gaban Kiwon Lafiyar Matakin Farko ta Jihar Taraba ƙarƙashin Shirin IMPACT, ta ƙaddamar da rarraba kayan...

Mafi Shahara