Kasuwanci
Gwamna Namadi Ya Bukaci Hadin Gwiwar Hukumar Kwastam Don Farfado Da Yankin Kasuwanci Na Maigatari
Gwamna Malam Umar Namadi na Jihar Jigawa ya jaddada kudirin gwamnatinsa na farfado da harkar kasuwanci mara shinge a Maigatari, wanda ya bayyana a matsayin muhimmin ginshikin bunkasar tattalin arziki, kasuwanci da masana’antu a jihar.
Ya bayyana hakan ne yayin wata ganawa da Kwamandan Yankin K da Jigawa na Hukumar Kwastam ta Najeriya, Kwamanda Dalhat Abubakar, wanda ya kai masa ziyarar ban girma a Fadar Gwamnati da ke Dutse.

Gwamna Namadi ya taya Kwamanda Abubakar murnar nadin nasa, tare da yaba wa hukumar Kwastam bisa goyon bayan manufofin cigaban jihar Jigawa, musamman wajen farfado da aikin Maigatari da aka yi watsi da shi.
Ya nuna godiya bisa goyon bayan Kwamandan ya bayar, tare da yabawa da rahotannin da ke nuna yadda yake hada kai da tawagar tattalin arzikin jihar kan aikin.
Gwamnan ya bayyana tarihin Maigatari Free Trade Zone, yana cewa ko da yake an kafa yankin fiye da shekaru 25 da suka wuce, an bar shi kara zube ba tare da cimma manufarsa ba.

Ya ce gwamnatinsa ta dauki matakai masu muhimmanci domin farfado da shi.
A cewarsa, an biya kudaden lasisi na doka, an yi shirin sake matsuguni ga mazauna yankin, kuma ana ci gaba da tattaunawa da masu zuba jari domin fara aiki da yankin.
Ya jaddada muhimmancin hadin gwiwa da hukumomin tarayya kamar Hukumar Kwastam don tabbatar da cewa yankin ya fara aiki gaba daya.

A nasa jawabin, Kwamanda Abubakar ya tabbatar da cewa Hukumar Kwastam ta shirya tsaf don fara aiki a Maigatari nan take, yana mai cewa sauran matsalolin da ke akwai na harkokin gudanarwa ne da na kayayyakin aiki, kuma za a iya magance su cikin sauki.
Ya yaba da jajircewar tawagar tattalin arzikin Jigawa, yana bayyana su a matsayin kwararru da kuma masu cikakken biyayya ga hangen nesan gwamna dangane da Maigatari.

Kwamanda Abubakar ya kuma jaddada irin fifikon da yankin Maigatari ke da shi, yana cewa kasancewarsa kusa da iyaka na ba shi gagarumar dama fiye da sauran yankuna, har da manyan cibiyoyin kasuwanci irin su Kano.
Ya bukaci ci gaba da hadin gwiwa tsakanin dukkan masu ruwa da tsaki don shawo kan sauran kalubale da kuma fitar da cikakken alfanu daga yankin.
A karshe, Gwamna Namadi ya tabbatar da cewa gwamnatinsa a shirye take ta dauki matakan da suka dace da shawarwari da tallafin da ake bukata don tabbatar da cewa Maigatari ya fara aiki gaba daya, tare da yin tasiri ga tattalin arziki.
Usman Muhammad Zaria
-
Labarai2 days agoIran ta Tabbatar da Kisan Ayatollah Khamenei a Hare-haren Amurka da Isra’ila
-
Labarai4 days agoMajalisar Dokokin Jihar Kaduna Ta Amince da Kasafin Kudin Kananan Hukumomin Jihar na 2026
-
Labarai4 days agoAzumin Ramadan: Shugaban Karamar Hukumar Birnin Kudu Ya Bada Tallafin Kudi ga Marasa Galihu
-
Labarai6 days agoUwargidan Gwamnan Zamfara Ta Kaddamar da Rabon Tallafin Ramadan ga Marasa Galihu
-
Labarai6 days agoWani Bam Kirar Hannu Ya Fashe a Kan Hanyar Gusau Zuwa Funtua
-
Labarai3 days agoBankin Raya Kasashen Afirka Zai Samar da Shirin Bunƙasa Aikin Noma a Jigawa
-
Labarai3 days agoGwamnatin Jigawa ta Gargadi ‘Yan Kwangila Kan Ingancin Abincin Ramadan
-
Labarai3 days agoMasarautar Hadejia ta Raba Zakkar Kayan Amfanin Gona da Dabbobi a Garin Unik
