Labarai
Dorinar Ruwa ta Yi Ajalin Mutane Biyu, ta Raunata Shida a Gombe
Mutanen garin Dadin-Kowa da ke Ƙaramar Hukumar Yamaltu Deba a Jihar Gombe, sun shiga damuwa kan yadda wata Dorinar ruwa ta addabi yankin, ta hanyar kashe mutane da kuma lalata gonaki.
Cikin watanni biyu, Dorinar ta kashe mutum biyu, ta karya wasu biyu, sannan ta jikkata wasu huɗu, waɗanda yawanci manoma da masunta ne a Dam ɗin Dadin-Kowa.
Matsalar ta sa ɗan Majalisar Tarayya na Yamaltu Deba, Inuwa Garba, ya kai koke gaban Majalisar Wakilai, inda ya nemi gwamnati ta hanzarta kawo wa mazauna yankin ɗauki.
Ya ce, “Ta’addancin Dorinar ya yi yawa. Idan ba a taimaka mana ba, za ta ci gaba da kashe mutane da lalata amfanin gona.”
A makon da ya gabata, Dorinar ta farmaki wani matashi mai suna Sama’ila Garba (Mai Lasa), bayan ya faɗa cikin ruwa.
Shaidu, sun ce dabbar ta yi ƙoƙarin kashe matashin, ta yadda hanjin cikinsa sai da ya fito, kafin a ceto shi.
Garba Zafi, ɗan uwansa, ya ce Sama’ila ya je bakin ruwa ne kawai sai ya ji ya faɗa, daga nan Dorinar ta afka masa.
Wani mazaunin garin, Akilu Gyara Sa’a, ya roƙi gwamnati ta kai musu agaji duba da yadda rayuwar mutane ke da muhimmanci.
Ya ce: “Dorinar tana lalata gonaki, tana kashe mutane. Gwamnati ta hanzarta magance matsalar kafin abin ya ta’azzara.”
Da aka tuntuɓi kakakin rundunar ’yan sandan jihar, DSP Buhari Abdullahi, ya ce zai bincika domin samun cikakken bayani kan lamarin.
Ya zuwa lokacin haɗa wannan rahoto bai yi ƙarin haske kan lamarin ba.
-
Labarai2 days agoIran ta Tabbatar da Kisan Ayatollah Khamenei a Hare-haren Amurka da Isra’ila
-
Labarai4 days agoMajalisar Dokokin Jihar Kaduna Ta Amince da Kasafin Kudin Kananan Hukumomin Jihar na 2026
-
Labarai6 days agoUwargidan Gwamnan Zamfara Ta Kaddamar da Rabon Tallafin Ramadan ga Marasa Galihu
-
Labarai4 days agoAzumin Ramadan: Shugaban Karamar Hukumar Birnin Kudu Ya Bada Tallafin Kudi ga Marasa Galihu
-
Labarai6 days agoWani Bam Kirar Hannu Ya Fashe a Kan Hanyar Gusau Zuwa Funtua
-
Labarai3 days agoBankin Raya Kasashen Afirka Zai Samar da Shirin Bunƙasa Aikin Noma a Jigawa
-
Labarai3 days agoGwamnatin Jigawa ta Gargadi ‘Yan Kwangila Kan Ingancin Abincin Ramadan
-
Labarai3 days agoMasarautar Hadejia ta Raba Zakkar Kayan Amfanin Gona da Dabbobi a Garin Unik
