Connect with us

Labarai

Ana Cigaba Da Ceto Mutanen Da Suka Makale Wajen Hakar Ma’adanai A Naija

Published

on

Masu aikin ceto sun ceto mutane bakwai da suka makale a wani wajen hakar ma’adanai a yankin Galadima Kogo da ke karamar hukumar Shiroro ta Jihar Neja.

Ministan ma’adanai, Dele Alake  ya bayyana hakan a wata sanarwa da mai taimaka masa na musamman kan harkokin yada labarai, Segun Tomori ya fitar ranar Talata a Abuja.

Ya ce an tura masu bayar da agaji zuwa wajen da lamarin ya faru, inda ya kara da cewa ana aikin ceton tare da hadin gwiwar kamfanin hakar ma’adanai.

Kamfanin dillancin labaran Nijeriya (NAN), ya ruwaito cewa kimanin  mutane 30 ne suke makale cikin ramin da ake hakar ma’adanai da wani ke aiki.

Kamfanin dillancin labaran na NAN ya kara da cewa Darakta-Janar na Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa na Jihar Neja (NSEMA)Alhaji Abdullahi Arah ya ce lamarin ya faru ne sakamakon mamakon ruwan sama.

Ministan ya ce kokarin da gwamnatin tarayya ke yi ya nuna yadda ta himmatu wajen ganin an dakile asarar rayuka, da kuma ceto wadanda suka makale.

Da samun labarin faruwar lamarin, sai muka tura jami’an kula da ma’adanai na tarayya (FMO) da jami’an hukumar binciken ma’adanai wajen domin ceto wadanda suka makale“.

Tare da hadin gwiwar kamfanin hakar ma’adanai, mun ceto mutane bakwai da suka makale, ana kuma ci gaba da gudanar da aikin ceto a wajen,” in ji shi.

Ya bada  tabbacin cewa gwamnatin tarayya ta kuduri aniyar yin bincike kan musabbabin afkuwar lamarin.

Labarai

Labarai15 hours ago

Hukumar Kula da Kogin Benuwe ta Dauki Matakin Yashe Laka da Yashi da ke Barazana ga Noman Rani

Ayyukan ban ruwa a yankin Kogin Benuwe na fuskantar barazana sakamakon taruwar Laka da Yashi a kogin, lamarin da ke...

Labarai1 day ago

Gwamna Namadi Ya Raba Tallafin Ramadan ga Ma’aikata da Marasa Galihu

Daga Usman Muhammad Zaria Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya raba tallafin kayan abinci na watan Ramadan tare da...

Labarai2 days ago

Sojoji Sun Yi Nasarar Kwato Dabbobi 257 da Aka Sace a Karamar Hukumar Gwarzo

Daga Abdullahi Jalaluddeen Sojojin Najeriya sun sami nasarar dawo da Shanu da Awaki  257 da aka sata a  wani aikin...

Labarai2 days ago

Uwargidan Gwamnan Zamfara ta Yaba da Yadda Aka yi Rabon Tallafin Ramadan

Daga Aminu Dalhatu  Uwargidan Gwamnan Jihar Zamfara, Hajiya Huriyya Dauda Lawal, ta yaba wa dukkan masu ruwa da tsaki bisa...

Labarai2 days ago

Gwamnatin Kebbi Za ta Raba Hatsi da Kayayyakin Aikin Gona ga Marasa Galihu

Daga Sani Dutsinma Gwamnatin Jihar Kebbi ta kammala shirye-shiryen raba kayayyakin aikin noma da nau’o’in hatsi daban-daban ga mutane miliyan...

Labarai2 days ago

Gwamnatin Kwara Ta Jaddada Kudurinta Na Kula Da Jin Daɗin Masu Harkar Sufuri

Gwamnatin Jihar Kwara ta bai wa masu harkar sufuri a jihar tabbacin ci gaba da kare muradunsu da jin daɗinsu....

Labarai2 days ago

Gwamnan Zamfara Ya Haramta Karbar Kudin Haraji A Hannu

Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya bayar da umarnin dakatar da duk wani tsarin karbar kuɗaɗen shiga ta tsabar kuɗi...

Labarai2 days ago

Gwamnatin Tarayya Ta Faɗaɗa Rijistar Tallafin Jama’a Domin Tantance Masu Buƙata

Gwamnatin Tarayya na faɗaɗa tare da ƙarfafa Rijistar Tallafin Jama’a ta Ƙasa National Social Register domin tabbatar da cewa an...

Labarai2 days ago

Gwamna Idris Ya Ba da Umarnin Binciken Gobarar da Ta Tashi a Makarantar Nurul Haqq da ke Birnin Kebbi

Gwamnan Jihar Kebbi, Nasir Idris, ya bayar da umarnin gaggauta kafa wani kwamitin bincike mai ƙarfi domin gano musabbabin gobarar...

Labarai2 days ago

Taraba Ta Kaddamar da Rarraba Kayan Aikin A Kananan Hukumomi 16

Hukumar Kula da Ci gaban Kiwon Lafiyar Matakin Farko ta Jihar Taraba ƙarƙashin Shirin IMPACT, ta ƙaddamar da rarraba kayan...

Mafi Shahara