Labarai
An Bai Wa Alhazan Jihar Naija Tabbacin Samun Kyakkyawar Kulawa Yayin Aikin Hajji
Alhazan jihar Neja sun samu tabbacin kyautata walwala da jin dadinsu yayin da suke kasa mai tsarki don gudanar da aikin hajjin bana.
Mataimakin gwamnan jihar, Kwamared Yakubu Garba ya ba da wannan tabbacin ga jirgin karshe na jigilar alhazan jihar daga filin jirgin sama na Bola Ahmad Tinubu da ke Minna zuwa birnin Madina na kasar Saudiyya.
Kwamared Yakubu Garba ya ce gwamnatin jihar Naija a karkashin jagorancin Gwamna Mohammed Umar Bago Alhazan jihar ta yi tanadi na musamman ga Alhazan domin samun kyakkyawar kulawar da ta da ce yayin gudanar da aikin hajjin bana ba tare da wata matsala ba.
Ya kuma yi kira ga Mahajjatan da su yi addu’a ga jihar Neja da kasa baki daya, domin fatan Allah Ya warware dukkan kalubalen da ake fuskanta.
A nasa jawabin Amirul Hajj na jihar kuma Sarkin Kagara, Ahmed Garba Gunna Attahiru na biyu, ya bayyana jin dadinsa bisa goyon baya da hadin kan da Gwamna Umar Bago ya ba su domin gudanar da aikinsu.
Ya ce a nasu bangaren mambobin tawagarsa za su yi duk mai yiwuwa don tabbatar da ganin sun sauke nauyin da aka daura musu.
Aliyu Lawal
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
-
Labarai6 days agoMasu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki
