Connect with us

Labarai

Sanata Yari Ya Raba Shanu 380 Ga Al’umma Domin Bikin Sallah

Published

on

Sanata mai wakiltar mazabar Zamfara ta yamma, Alhaji Abdulaziz Yari Abubakar ya fara rabon shanu 380 ga mazabun siyasa 147 a kananan hukumomi 14 na jihar.

Da yake kaddamar da shirin rabon shanun da aka gudanar a Unguwar Kasuwar Daji da ke karamar Hukumar Kauran Namoda, shugaban kwamitin rabon Alhaji Lawal Liman Gabɗon Mattaura ya bayyana cewa, hakan na daga cikin karramawar Sanata Yari ga shuwagabanni da masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC a jihar.

Lawal Liman wanda kuma shi ne shugaban kungiyar siyasar Sanatan ya ce kowace Unguwa za ta karbi shanu biyu domin gudanar da bukukuwan Sallah cikin farin ciki.

            Shugabannin kwamitin rabo

 

Shugaban wanda ya samu wakilcin dan kwamitin, Muhammad Muttaka Rini (Makaman Zamfara), ya bayyana cewa, Gundumomin da ke karkashin kananan hukumomi 4 da suka hada da Kaura Namoda, Zurmi, Shinkafi da Birnin Magaji da suka hada mazabar Sanatan Zamfara ta Arewa sun karbi kason su.

A cewarsa, sauran unguwannin kananan hukumomi 10 da ke karkashin mazabar Zamfara ta tsakiya da Zamfara ta yamma za su karbi nasu rabon ne tsakanin ranakun Litinin zuwa Talatar wannan makon.

A yayin da yake yabawa da irin namijin kokarin da Sanata Abdulaziz Yari Abubakar ya yi na yi wa al’ummarsa hidim, shugaban ya yi kira ga sauran shugabannin siyasar jihar da su yi koyi da irin wannan karamcin da nufin tabbatar da zaman lafiyar  al’umma da inganta  tattalin arzikin  don rage musu radadi.

Shugaban ya kuma yi kira ga al’ummar Musulmi musamman na jihar da wadanda suka je aikin Hajji da su yi amfani da wannan kwanaki goma na Zulhijja wajen karfafa addu’o’in samun zaman lafiya da kwanciyar hankali a jihar da kasa baki daya.

 

Sani Dutsinma

Labarai

Labarai20 hours ago

Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu

Daga Nasir Malali  Dakarun Sashe na biyu na Rundunar Haɗin Gwiwa ta Arewa maso Yamma, Operation FANSAN YAMMA, sun ceto...

Labarai22 hours ago

NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta

Daga Yusuf Zubairu, Kaduna Hukumar Raya Yankin Arewa Maso Yamma ta bayyana dawo da tsaro a matsayin babban fifikonta a...

Labarai5 days ago

Gwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, zai halarci zama na 81 na Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya...

Ilimi6 days ago

An Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo

Daga Khadijah Aliyu  Karamar Hukumar Gwarzo ta Jihar Kano ta raba kayan makaranta guda 20,243 ga ɗaliban makarantun firamare daban-daban...

Labarai1 week ago

Gwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027

Daga Usman Muhammad Zaria  Gwamnatin Jihar Jigawa ta sake jaddada aniyarta ta ci gaba da aiki kafada da kafada da...

Labarai1 week ago

Mataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya

Daga Bello Wakili, Abuja Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya dawo Najeriya bayan ya wakilci Shugaba Bola Ahmed Tinubu a...

Labarai1 week ago

UNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina

Daga Isma’il Adamu, Katsina Asusun Tallafawa Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya, UNICEF, tare da haɗin gwiwar Hukumar Ilimin Firamare ta...

Labarai1 week ago

NSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Hukumar Tsaro Farin kaya ta Najeriya, NSCDC, reshen Jihar Zamfara, ta kama wani mutum mai shekaru...

Labarai1 week ago

Majalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari

Daga KHADIJAH ALIYU, Kano Majalisar Dokokin Jihar Kano ta yi kira ga gwamnatin jihar da ta tabbatar da kammala aikin...

Labarai1 week ago

Masu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki

Daga ALI MUHAMMAD RABIU Shirin Ƙarfafa Juriya Ga Sauyin Yanayi A Yankunan Busassun yankuna na Jihar Kwara, KWACReSAL, ya fara...

Mafi Shahara