Labarai
Hukumar Alhazai Ta Jihar Kwara Ta Jajantawa Iyalan Alhazan Da Suka Rasu
Hukumar Alhazai ta jihar Kwara ta jajantawa iyalan wasu alhazai biyu da suka rasu a birnin Madina na kasar Saudiyya.
A cikin wata sanarwa da sakataren zartarwa na hukumar jin dadin alhazai ta jihar Alhaji Abdulkadir Abdulsalam Ya fitar, ya ce Saliu Mohammed, wanda ya zo a sahu na 3 na alhazan har, ya rasu ne a sashin kula da marasa lafiya na wani asibitin gwamnati da ke Madina.
Ya ce Hajiya Hawawu Mohammed da ke cikin rukuni na 9 kuwa, ta rasu ne biyo bayan fadowa daga saman benen masaukinsu da ke Madina.
Alhaji Abdulsalam ya ce hukumar alhazai na cike da alhinin wannan lamarin, ta kuma mika ta’aziyya ga iyalansu tare da yi musu addu’ar Allah ya jikan su da Aljannar Firdausi.
Ali Muhammad Rabi’u
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
