Connect with us

Labarai

Mahajjata Sun Yabawa Gwamnatin Borno Da Hukumar Alhazai Bisa Basu Abinci Mai Inganci

Published

on

Alhazan Jihar Borno  sun yabawa hukumar alhazai ta kasa (NAHCON) da gwamnatin jihar Borno bisa kyakkyawan tsarin shirin ciyarwa  a  Makka da Madina.

Alhazan da a halin yanzu suke shirin fara aikin Hajji a ranar Juma’a ta makon gobe, sun bayyana gamsuwarsu da inganci da wadataccen abinci da ake basu a kullum.

Wakilinmu Dauda Iliya wanda yanzu haka yake a garin Makka ya ruwaito cewa Alhazai 1,646 daga cikin 1,815 daga jihar sun kammala zamansu a Madina bayan sun yi ziyara a muhimman wurare.

Daya daga cikin mahajjatan  Hajia Fatima Usman ta ce ana basu abincin  mai gina jiki kuma irin wanda suka saba da shi.

Abincin da muke samu tun daga Madina zuwa nan Makka yana da kyau kwarai da gaske, muna jin dadin yadda ake bamu abincinmu na gargajiya da muka saba da shi, muna godiya ga Hukumar NAHCON da Gwamnatin Jihar Borno da suka tabbatar mana da samun wadataccen abinci a wannan lokacin.” in ji Hajiya Fatima.

Wani Alhaji mai suna Malam Abba Kyari, ya yabawa jami’an kwamitin ciyar da abinci da masu ba da abinci bisa kwarewa da kuma kula da Alhazai.

Kyari ya ce “Ma’aikatan da ke kula da abinci suna matukar bibiyar bukatunmu da korafe-korafenmu, idan akwai. Suna tabbatar da cewa an ba mu abinci a kan lokaci“.

Shugaban kwamitin ciyarwa  na tawagar Amirul Hajj Dr Ibrahim Adam ya bayyana jin dadinsa bisa yabon da Alhazan  ke yi, yana mai cewa hakan ya nuna irin jajircewar da gwamnatin jihar ta yi na kyautata rayuwar jami’ar ta da suke gudanar da aikin Hajjin.

Dangane da korafin da wasu maniyyatan ke yi na rasa abincin, Dr Ibrahim ya ce kwamitin ya bukaci masu kula da abincin da su kara samar da wadataccen abincin a lokacin karin kumallo da kuma abincin dare domin tabbatar da cewa  kowa ya samu.

Abin da muka sa a gaba shi ne tabbatar da kula da mahajjatan mu a yayin wannan tafiya ta ibada. Yabo daga alhazan Borno ya nuna cewa muna kan turbar da ta dace, kuma za mu ci gaba da hada hannu da NAHCON wajen tabbatar da wannan tsari,” in ji Dokta Ibrahim.

Wakilinmu ya ruwaito cewa, ana sa ran za a yi jigilar alhazan jihar Borno na karshe a kasa mai tsarki nan da kwanaki biyu masu zuwa.

Dauda Iliya

Labarai

Labarai4 days ago

Gwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, zai halarci zama na 81 na Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya...

Ilimi5 days ago

An Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo

Daga Khadijah Aliyu  Karamar Hukumar Gwarzo ta Jihar Kano ta raba kayan makaranta guda 20,243 ga ɗaliban makarantun firamare daban-daban...

Labarai6 days ago

Gwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027

Daga Usman Muhammad Zaria  Gwamnatin Jihar Jigawa ta sake jaddada aniyarta ta ci gaba da aiki kafada da kafada da...

Labarai6 days ago

Mataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya

Daga Bello Wakili, Abuja Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya dawo Najeriya bayan ya wakilci Shugaba Bola Ahmed Tinubu a...

Labarai6 days ago

UNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina

Daga Isma’il Adamu, Katsina Asusun Tallafawa Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya, UNICEF, tare da haɗin gwiwar Hukumar Ilimin Firamare ta...

Labarai6 days ago

NSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Hukumar Tsaro Farin kaya ta Najeriya, NSCDC, reshen Jihar Zamfara, ta kama wani mutum mai shekaru...

Labarai6 days ago

Majalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari

Daga KHADIJAH ALIYU, Kano Majalisar Dokokin Jihar Kano ta yi kira ga gwamnatin jihar da ta tabbatar da kammala aikin...

Labarai6 days ago

Masu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki

Daga ALI MUHAMMAD RABIU Shirin Ƙarfafa Juriya Ga Sauyin Yanayi A Yankunan Busassun yankuna na Jihar Kwara, KWACReSAL, ya fara...

Ilimi7 days ago

Zamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta

Daga Aminu Dalhatu  Hukumar Ilimin Bai-daya ta Jihar Zamfara, ZSUBEB, ta kaddamar da shirin shigar da yara makaranta na shekarar...

Labarai1 week ago

Gwamnan Kebbi Ya Yabi WAMY Kan Jinya Kyauta Ga Marasa Lafiya

Daga Sani Dutsinma Gwamnan Jihar Kebbi, Nasir Idris, ya yaba wa Ƙungiyar Matasa Musulmi ta Duniya (WAMY) kan shirya aikin...

Mafi Shahara