Labarai
Jihar Kwara Ta Kammala Jigilar Alhazan Bana
Kashi na karshe na Mahajjata Dari uku da hudu daga jihar Kwara da babban birnin tarayya Abuja sun isa kasar Saudiyya domin gudanar da aikin hajjin bana.
An dauki mahajjatan ne a jirgin Air Peace Air craft APK7944 ta filin jirgin sama na Ilorin da misalin karfe 3 na daren Juma’a zuwa Madina.
Jirgin na kunshe da Mahajjatan jihar Kwara 286, da kuma Alhazai da ragowar Alhazai da jami’an hukumar alhazai na babban birnin tarayya su 18.
Hakan ya kawo karshen jigilar Alhazai dubu uku da dari daya da biyu daga shiyyar Kwara, wanda ya kunshi jihar Kwara, Ondo da kuma Ekiti.
A jiya Juma’a ne Alhazan suka gudanar da zanga-zangar lumana don nuna bacin ransu kan jinkirin da aka samu na jigilarsu tun ranar Alhamis.
Ali Muhammad Rabi’u
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
