Kasuwanci
An Share Filin Noma Kadada 100 Don Karfafa Matasa Su Yi Noma A Babura Jihar Jigawa
Shugaban karamar hukumar Babura ta jihar Jigawa, Malam Hamisu Muhammad Garu, ya kaddamar da shirin karfafa aikin gona da nufin sanya matasa aikin noman shinkafa a wani bangare na kokarin inganta ayyukan yi da samar da abinci a yankin.
Da yake jawabi yayin bikin kaddamar da aikin aka gudanar a garin Babura, shugaban ya bayyana cewa, Gwamna Malam Umar Namadi ne ya bullo da shirin a matsayin wani muhimmin mataki na samar da guraben ayyukan yi ga matasa, da habaka tattalin arzikin kananan hukumomi, da karfafa samar da abinci a fadin jihar.
A cewarsa, gwamnatin jihar ta samar da muhimman kayayyakin amfanin gona da suka hada da takin zamani, magungunan kashe kwari, irin shinkafa mai yawan gaske, da injinan feshi.
Malam Hamisu Garu ya yi nuni da cewa, za a raba kayayyakin ga matasa 200 da aka zabo daga sassa daban-daban na karamar hukumar.
Ya kara da cewa, karamar hukumar ta ware tare da share fili mai fadin hekta 100 domin fara aikin.
Shugaban ya nuna jin dadinsa ga gwamnatin jihar da ta fara shirin.
Ya ce, shirin zai hana matasa yin kaura zuwa birane domin neman ayyukan yi, lamarin da yakan jefa su cikin hatsari da kuma gurgunta makomarsu.
A nasa jawabin, babban daraktan cibiyar bincike ta jiha Dakta Suleman Rufa’i, ya bayyana shirin a matsayin wani kokari na farko, inda ya kara da cewa akwai shirye-shiryen kara fadada shi bisa burin gwamnati na mayar da jihar Jigawa a matsayin jihar da ke kan gaba wajen samar da abinci a Nijeriya.
Rediyon Nijeriya ya ruwaito cewa, sarakunan gargajiya da suka halarci taron sun hada da Hakimin Babura, Sarkin Ban Ringim, Alhaji Muhammad Nata’ala Mustapha, da Hakimin Garu, Dan-makwayon Ringim, Alhaji Suhailu Abubakar Usman, sun yabawa gwamnati kan wannan shiri.
Shugabannin sun bukaci wadanda suka ci gajiyar shirin su nuna kishin kasa da alhaki ta hanyar amfani da tallafin yadda ya kamata domin tabbatar da nasarar shirin.
USMAN MZ/Dutse
-
Labarai3 days agoIran ta Tabbatar da Kisan Ayatollah Khamenei a Hare-haren Amurka da Isra’ila
-
Labarai4 days agoMajalisar Dokokin Jihar Kaduna Ta Amince da Kasafin Kudin Kananan Hukumomin Jihar na 2026
-
Labarai4 days agoAzumin Ramadan: Shugaban Karamar Hukumar Birnin Kudu Ya Bada Tallafin Kudi ga Marasa Galihu
-
Labarai7 days agoUwargidan Gwamnan Zamfara Ta Kaddamar da Rabon Tallafin Ramadan ga Marasa Galihu
-
Labarai6 days agoWani Bam Kirar Hannu Ya Fashe a Kan Hanyar Gusau Zuwa Funtua
-
Labarai4 days agoBankin Raya Kasashen Afirka Zai Samar da Shirin Bunƙasa Aikin Noma a Jigawa
-
Labarai1 day agoGwamna Namadi Ya Raba Tallafin Ramadan ga Ma’aikata da Marasa Galihu
-
Labarai4 days agoMasarautar Hadejia ta Raba Zakkar Kayan Amfanin Gona da Dabbobi a Garin Unik
