Connect with us

Fasaha

An Nada Shugaban Hukumar Fasahar Sadarwa Da Inganta Tattalin Arziki Ta Jihar Jigawa

Published

on

Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya amince da nadin Dr. Mohammed Hassan a matsayin Darakta Janar na farko na Hukumar Fasahar Sadarwa da inganta Tattalin Arzikin ta fasahar zamani ta Jihar Jigawa.

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Sakataren Gwamnatin Jihar Jigawa, Malam Bala Ibrahim, ya fitar a Dutse.

Kafin nadin nasa, Dr. Muhammad Hassan shi ne shugaban hukumar Fasahar Sadarwa da Kimiyya ta Jigawa, wato Galaxy ITT.

Malam Bala Ibrahim ya bayyana cewa sabo  shugaban hukumar ya sami digirinsa na farko a fannin Lissafi daga Jami’ar Bayero, Kano, a shekarar 2008. Daga bisani, ya samu digiri na biyu a fannin Kimiyyar Kwamfuta daga Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Afirka (AUST), Abuja, a shekarar 2011, sannan ya ci gaba da karatu har ya samu digirin digirgir (Ph.D) a fannin Kimiyyar Kwamfuta da Injiniyanci daga Jami’ar Aizu da ke kasar Japan, a 2018.

Haka nan, Gwamnan ya amince da naɗin Baffajo Beita a matsayin sabon shugaban Galaxy ITT.

Kafin naɗinsa, Beita  Babban Jami’in Bayanan Fasaha ne a Galaxy Backbone da ke Abuja. Yana da ƙwarewa mai zurfi a fannin fasahar sadarwa, musamman a tsarin gudanar da cibiyoyin sadarwa, tsaro na yanar gizo, da ƙirƙirar fasahar yanar gizo.

Beita ya kammala digirinsa na farko a fannin Kwamfuta daga Jami’ar Anglia Ruskin, kuma ya fara aikinsa ne a Makarantar Informatics ta Jihar Jigawa da ke Kazaure, kafin ya taka muhimmiyar rawa a manyan ayyukan fasahar sadarwa a Turai, Gabas ta Tsakiya, da Afirka (EMEA) a fannoni daban-daban, ciki har da masana’antar mai da gas, da sarrafa kayayyaki, da harkokin kuɗi”.

Bugu da ƙari, Gwamnan ya amince da naɗin Muhammad Nura Zubairu a matsayin Daraktan Zartarwa na Ayyukan Fasaha, da Umar Ibrahim Gumel a matsayin Daraktan Zartarwa na Harkokin Kasuwanci a  Galaxy ITT.

Kafin wannan matsayi, Muhammad Nura ya kasance Injiniyan Tallafin Sadarwa a Galaxy ITT, kuma ya kammala babbar difloma (HND) a fannin Tattalin Arzikin Hadin Gwiwa da Gudanarwa daga Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Kano a shekarar 2010.

“Wadannan muhimman nade-nade na cikin shirye-shiryen Gwamna Namadi na ƙarfafa tattalin arzikin  Jihar Jigawa ta fasahar zamani, domin tabbatar da cewa hukumar na da kwararrun shugabanni da za su jagoranci kirkire-kirkire da inganta ayyukan fasahar sadarwa  a ciki da wajen jihar” in ji SSG.

Malam Bala Ibrahim ya ƙara da cewa an zaɓi waɗanda aka naɗa ne bisa cancanta, ƙwarewa, da nagarta.

Ya bukaci dukkan waɗanda aka naɗa da su yi aiki tukuru don aiwatar da manufofi da shirye-shiryen gwamnati bisa kyakkyawan.

Sanarwar ta ƙara da cewa, dukkan waɗannan nade-naden sun fara aiki ne nan take.

 

Usman Muhammad Zaria

 

 

Labarai

Labarai4 hours ago

Hukumar Kula da Kogin Benuwe ta Dauki Matakin Yashe Laka da Yashi da ke Barazana ga Noman Rani

Ayyukan ban ruwa a yankin Kogin Benuwe na fuskantar barazana sakamakon taruwar Laka da Yashi a kogin, lamarin da ke...

Labarai1 day ago

Gwamna Namadi Ya Raba Tallafin Ramadan ga Ma’aikata da Marasa Galihu

Daga Usman Muhammad Zaria Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya raba tallafin kayan abinci na watan Ramadan tare da...

Labarai1 day ago

Sojoji Sun Yi Nasarar Kwato Dabbobi 257 da Aka Sace a Karamar Hukumar Gwarzo

Daga Abdullahi Jalaluddeen Sojojin Najeriya sun sami nasarar dawo da Shanu da Awaki  257 da aka sata a  wani aikin...

Labarai1 day ago

Uwargidan Gwamnan Zamfara ta Yaba da Yadda Aka yi Rabon Tallafin Ramadan

Daga Aminu Dalhatu  Uwargidan Gwamnan Jihar Zamfara, Hajiya Huriyya Dauda Lawal, ta yaba wa dukkan masu ruwa da tsaki bisa...

Labarai1 day ago

Gwamnatin Kebbi Za ta Raba Hatsi da Kayayyakin Aikin Gona ga Marasa Galihu

Daga Sani Dutsinma Gwamnatin Jihar Kebbi ta kammala shirye-shiryen raba kayayyakin aikin noma da nau’o’in hatsi daban-daban ga mutane miliyan...

Labarai1 day ago

Gwamnatin Kwara Ta Jaddada Kudurinta Na Kula Da Jin Daɗin Masu Harkar Sufuri

Gwamnatin Jihar Kwara ta bai wa masu harkar sufuri a jihar tabbacin ci gaba da kare muradunsu da jin daɗinsu....

Labarai1 day ago

Gwamnan Zamfara Ya Haramta Karbar Kudin Haraji A Hannu

Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya bayar da umarnin dakatar da duk wani tsarin karbar kuɗaɗen shiga ta tsabar kuɗi...

Labarai1 day ago

Gwamnatin Tarayya Ta Faɗaɗa Rijistar Tallafin Jama’a Domin Tantance Masu Buƙata

Gwamnatin Tarayya na faɗaɗa tare da ƙarfafa Rijistar Tallafin Jama’a ta Ƙasa National Social Register domin tabbatar da cewa an...

Labarai1 day ago

Gwamna Idris Ya Ba da Umarnin Binciken Gobarar da Ta Tashi a Makarantar Nurul Haqq da ke Birnin Kebbi

Gwamnan Jihar Kebbi, Nasir Idris, ya bayar da umarnin gaggauta kafa wani kwamitin bincike mai ƙarfi domin gano musabbabin gobarar...

Labarai1 day ago

Taraba Ta Kaddamar da Rarraba Kayan Aikin A Kananan Hukumomi 16

Hukumar Kula da Ci gaban Kiwon Lafiyar Matakin Farko ta Jihar Taraba ƙarƙashin Shirin IMPACT, ta ƙaddamar da rarraba kayan...

Mafi Shahara