Kasuwanci
Gwamnatin Tarayya Za Ta Kafa Ka’idoji Ga Samar da Injinan Noma a Najeriya
Gwamnatin Tarayya ta ce za ta kafa ka’idoji da jagorori da za su tsara samarwa da amfani da injinan noma a fadin Najeriya.
Ministan Noma, Sanata Abubakar Kyari, ya bayyana haka a taron shekara-shekara na 45 na Ƙungiyar Injiniyoyin Noma ta Najeriya (NIAE), mai taken “Kafa Ka’idoji da Ƙarfafa Fasahohin da Aka Gwada Don Samar da Abinci da Ƙara Darajar Kayayyaki a Najeriya”, da aka gudanar a Ilorin.
Ya ba da shawarar kafuwar cibiyoyin injinan noma a kowanne yanki na ƙasa, domin horo, gyara, da tsara fasahohin aikin gona.
A cewarsa, bayan samun injina, mafi muhimmanci shi ne kafa tsarin daidaitawa, haɗa na’urori a gida, da tsarin kulawa, domin tabbatar da cewa kowanne injin da aka tura yana dacewa da aikin da aka tsara, tare da samun ƙwararrun masu gyara.
Ministan ya bayyana cewa, manoma na Najeriya suna bukatar fasahohi na gida, waɗanda aka haɓaka bisa fahimtar ƙasa, irin amfanin gona, da kuma girman noman da ake yi.
END/ALI MUHAMMAD RABIU
-
Ilimi6 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai5 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
-
Labarai1 day ago
Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu
-
Labarai1 day ago
NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta
