Kasuwanci
An Bayyana Ranar Karshe Ta Biyan Kudin Aikin Hajji Mai Zuwa
Hukumar Kula da jin dadin mahajjan Jihar Taraba ta bayyana 1 ga Disamba, 2025, a matsayin ranar ƙarshe ga masu niyyar yin hajji don kammala biyan kuɗin tafiyar hajji ta shekarar 2026.
A cewar wata sanarwa da Sashen Bayani na Hukumar ya fitar ta bakin Mataimakin Daraktan Hamza Baba Muri, an ƙayyade sabon kuɗin hajjin 2026 a Naira miliyan 7,630,000, kamar yadda Hukumar Hajj ta Kasa (NAHCON) ta amince.
Hukumar ta yi kira ga duk masu shirin yin hajji ta wannan tsari su tabbata sun biya kuɗin gaba ɗaya kafin ƙarshen wa’adin domin samun tabbacin shiga cikin masu sauke farali shekara mai zuwa.
Mai magana da yawun Hukumar ya jaddada cewa dukkan biyan kuɗi dole ne a yi su ta hannun Jami’an Cibiyoyin da aka keɓe, yana mai gargadin cewa ba za a karɓi korafi ba bayan wa’adin ƙarshe.
Ya bayyana cewa biyan kuɗi a kan lokaci zai bai wa Hukumar damar tattara jerin sunayen fasinjojin ƙarshe da kuma tura kuɗaɗen zuwa NAHCON bisa jadawalin ƙasa.
Haka kuma, mai magana da yawun Hukumar ya ce ana ci gaba da tattaunawa da masu samar da ayyuka a Saudi Arabia domin tabbatar da abinci mai inganci da wuraren kwana ga fasinjoji a Makkah yayin hajjin 2026.
Hukumar ta sake jaddada kudirinta na samar da mafi kyawun ayyuka ga fasinjojin Taraba, bisa manufa da burin Gwamnatin K-move.
END/JAMILA ABBA
-
Ilimi6 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai5 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
-
Labarai21 hours ago
Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu
-
Labarai23 hours ago
NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta
