Kasuwanci
Gwamnatin Jihar Nasarawa Ta Shirya Faɗaɗa Gonakin Shinkafar Jangwa Don Ƙara Samar da Shinkafa
Gwamnatin Jihar Nasarawa ta bayyana shirin ta na faɗaɗa gonakin shinkafar Jangwa daga hektar 3,300 zuwa hektar 5,000 a kakar noma mai zuwa, domin haɓaka samar da shinkafa da kuma ƙarfafa tattalin arziki a jihar.
Gwamna Abdullahi Sule ya bayyana haka yayin ziyarar duba girbin shinkafa a garin Jangwa, ƙaramar hukumar Awe.
Gwamnan ya ce faɗaɗa gonakin zai ƙara hektar 3,000 daga yawan da ake da shi yanzu, domin inganta ci gaban tattalin arziki ta hanyar aikin gona. Ya kuma nuna yadda jihar ta samu ci gaba a fannin noma, inda gonar ta faɗaɗa daga hektar 2,000 a bara zuwa hektar 3,300 a wannan shekarar.
Gwamna Sule ya sanar da haɗin gwiwar gwamnatin jihar da kamfanin Silvex International, babban kamfani mai sarrafa shinkafa, domin ƙara samar da shinkafa a jihar.
A cewar Gwamna Sule, haɗin gwiwar zai baiwa Silvex International damar sayen shinkafar kai tsaye daga gonakin jihar sannan a tattara ta a ƙarƙashin tambarin Nasarawa Agro-Commodity Company (NASACCO).
Shinkafar, wacce za a kaita Kasuwa da suna “NASACCO Gold”, ana sa ran zai ƙara shahara da darajar kayan shinkafar jihar a kasuwa.
Gwamnan ya yi godiya ga Silvex International bisa wannan haɗin gwiwa, wanda ya ce yana daga cikin matakan gwamnatinsa na jawo jarin masu zaman kansu zuwa fannin aikin gona a jihar.
Haka kuma, Gwamna Sule ya ce haɗin gwiwar zai taimaka wajen ƙara samar da shinkafa a jihar, tare da shirin faɗaɗa gonar zuwa hektar 8,000 nan gaba.
Gwamnan ya yaba wa matasa da al’ummomin garuruwan Jangwa, Ayakeke, da Agwatashi bisa jajircewarsu wajen tabbatar da nasarar gonar.
A nasa jawabi, Babban Jami’in Gudanarwa na Silvex International kuma Shugaban Aikin NASACCO, Abubakar Garba Ibrahim, ya bayyana haɗin gwiwar a matsayin babban ci gaba ga kamfanin.
Ya bayyana cewa haɗin gwiwar zai amfani jihar ta hanyoyi da dama, ciki har da haraji, ƙara darajar kayayyaki, da raba riba ta ƙarshe.
Aliyu Muraki, Lafia.
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
