Kasuwanci
Gwamna Yusuf Ya Gwangwaje Kano Pillars Da Sabbin Motocii
Gwamnatin Jihar Kano ƙarƙashin jagorancin Gwamna Alhaji Abba Kabir Yusuf ta bai wa ƙungiyar kwallon ƙafa ta Kano Pillars Football Club sabbin motoci uku domin sauƙaƙa musu matsalolin sufuri a yayin gasar Premier ta shekarar 2025/2026 da ke gudana.
Motocin sun haɗa da babbar motar Marcopolo mai kujeru 29 don ɗaukar ’yan wasa, motar samfurin Hummer, da kuma Sharon da za a yi amfani da ita wajen harkokin gudanarwa da sufuri.
A lokacin da yake mika makullai da takardun motocin a madadin Gwamnan, Sakataren Gwamnatin Jihar Kano, Malam Ibrahim Umar Farouk, ya roƙi matasan jihar masu son wasanni da su ci gaba da zama masu bin doka da oda tare da guje wa duk wani abu da zai bata sunan jihar.
Ya bayyana cewa wannan kyauta ta nuna yadda Gwamna Yusuf ke da ƙwarin gwiwa wajen ƙarfafa matasa da bunƙasa harkokin wasanni a jihar.
A nasa jawabin, Kwamishinan Matasa da Wasanni, Mustapha Kwankwaso, ya bayyana godiyarsa ga Gwamna Yusuf bisa wannan babban ci gaba da zai ƙara wa ’yan wasan kwarin gwiwa da jin daɗin aiki.
Ya kuma yi kira ga magoya bayan ƙungiyar Sai Masu Gida da su kasance masu ladabi da biyayya tare da ci gaba da nuna goyon baya cikin lumana.
Da yake mayar da martani, Manajan Janar na Kano Pillars FC kuma kyaftin ɗin Super Eagles, Ahmed Musa (MON, OON), ya yaba wa Gwamna Yusuf bisa goyon baya da ƙaunar da yake nuna wa ƙungiyar.
Ahmed Musa ya kuma roƙi gwamnatin jihar da ta ba da girmamawa ta musamman ga tsohon kyaftin ɗin ƙungiyar, Rabiu Ali, domin tunawa da gudunmawar da ya bayar wajen bunƙasa kwallon ƙafa a Najeriya, yana mai kiran sa da “ɗaya daga cikin fitattun ’yan wasa mafiya tasiri da suka taka leda a tarihin NPFL.”
A halin yanzu, ƙungiyar Kano Pillars za ta karɓi bakuncin Niger Tornadoes ta Minna a wasansu na ranar goma ta gasar NPFL a wannan Asabar, a filin wasa da suka ɗauka a matsayin gida na wucin gadi — Filin Muhammadu Dikko da ke Katsina.
Khadijah Aliyu
-
Ilimi6 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
-
Labarai1 day ago
Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu
-
Labarai1 day ago
NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta
