Ilimi
Kwamishinan Ilimi Na Kano Ya Yi Kira Da A Karfafa Shugabancin Makarantu Domin Inganta Karatun Dalibai
Kwamishinan Ilimi na Jihar Kano, Dr. Ali Haruna Abubakar Makoda, ya jaddada muhimmancin samun ƙwararrun shugabannin makarantu wajen inganta koyarwa da haɓaka sakamakon karatu a fadin makarantun jihar.
Wannan bayanin na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Daraktan Wayar da Kai na Ma’aikatar Ilimi, Kwamared Balarabe Abdullahi Kiru, ya sanya wa hannu.
Kwamishinan ya bayyana hakan ne a wajen taron horaswa na kwanaki biyu mai taken “Leading Learning for Gender Equality in Education” wanda British Council ta shirya domin wakilai daga jihohin Kano, Kaduna, Plateau da kuma Babban Birnin Tarayya Abuja (FCT).
Dr. Makoda ya ce, jagoranci mai ƙarfi da tsari a cikin makarantu shi ne ginshiƙin cimma ingantaccen ilimi. Ya kara da cewa, shugabannin makarantu su dinga tsara ayyuka yadda ya kamata, su rika sa ido kan darussa, da kuma gano wuraren da malamai ke buƙatar ƙarin horo ko ƙwarewa.
Ya kuma jaddada buƙatar jagoranci da ba da ƙarfafawa ga malamai a kai a kai, yana mai cewa gwamnatin jihar na da cikakken shirin ci gaba da horas da malamai a matakin firamare da sakandare, tare da tabbatar da cewa ana biyan su albashi kafin ko a ranar 25 ga kowane wata.
Kwamishinan ya gode wa British Council bisa shirya wannan taro, sannan ya shawarci shugabannin makarantu da malamai da su nuna godiya ta hanyar yin aiki tukuru domin ƙara bunƙasa tsarin ilimi a Jihar Kano.
Abdullahi Jalaluddeen, Kano
-
Ilimi6 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
-
Labarai1 day ago
Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu
-
Labarai1 day ago
NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta
