Ilimi
Hukumar Bunkasa Ilimin Manyan Makarantu Ta Shirya Taro Na Musamman Ga Jami’anta
Hukumar bunkasa ilimin gaba da sakandare ta jihar Jigawa ta shirya taron tattaunawa ga jami’an gudanar da shirin koyawa dalibai musamman wadanda suke da nakasu a jarrabawar NECO ko WAEC wato Remedial program don su sami nasarar cin jarrabawar da za ta basu damar ci gaba da karatu a makarantun gaba da sakandare.
Da yake jawabi a wajen taron, Shugaban hukumar, Dr Abbas A Abbas ya bayyana cewar gwamnatin jihar jigawa karkashin jagorancin Malam Umar Namadi ta sahalewa hukumar gudanar da shirin da ta saba yi duk shekara wajen baiwa daliban da suka fadi a jarrabawar NECO ko WAEC koyarwa ta musamman.
Yana mai cewar, sahalewar na da nufin basu damar sake rubuta jarrabawar don su sami dukkanin abun da ake bukata da zai basu damar ci gaba da karatun gaba da sakandare.
Dr Abbas A Abbas yace wannan shirn daya ne daga irin shirye shiye guda 6 da hukumar ke gudanarwa wanda doka ta basu dama.
Ya kuma kara da cewar, makasudin wannan tattaunawar shine a zaburar da jami’an kan irin aikin dake gaban su na ilimantar da dalibai hanyoyin da za su bi wajen amsa tambayoyin da akeyi a jarrabawar NECO ko WAEC.
Yace hakance tasa hukumar ta gayyato kwararrun masana don su kara bayar da bita ga jami’an a fannonin jarrabawar da ta shafi turanci da lissafi da kuma irin kalubalen da dalibai kan fuskanta wajen amsa tambayoyin alokacin jarrabawa.

Dr Abass ya kuma yabawa Gwamna Umar Namadi wajen kokarin sa na bunkasa harkar ilimi wanda daya ne daga cikin kudure kuduren sa 12 na ciyar da jihar gaba.
A jawaban su daban daban, kwararriya mai baiwa Gwamna shawara a Basic Education, Dr Hauwa Mustapha Babura da mataimaki na musamman ga Gwamna a fannin ilimin manya, Alhaji Garba Makama Gwaram sun yabawa Gwamna Namadi bisa kokarin sa na tallafawa shirin da sauran shirye-shiryen da hukumar bunkasa ilimin manya ke gudanarwa don baiwa daliban da suka fadi a jarrabawa damar sanin makamar da za su sami damar sake yin wata jarrabawar.
Sun kuma yi kira ga Jami’an da zasu gudanar da shirin da su saka tsoron Allah da kishin taimakawa daliban don cimma nasarar da aka sa a gaba.
Kazalika, sun yabawa kokarin Baban sakataren gudanarwa na hukumar Dr Abbas A Abbas bisa jajircewar sa wajen habaka ilimin manya a fadin jihar Jigawa.
Radio Nigeria ya bamu rahoton cewar, a lokacin taron an gudanar da takardu daban-daban a kan sabbin dabarun da za’a bi don tallafawa daliban da basu damar sake rubuta jarrabawar musamman a fannin turanci da lissafi da kuma shawarwariin da za ayi amfani dssu don kwalliya ta biya kufin sabulu.
Fiye da jami’ai masu hiror da dalibai 131 ne da aka gayyata daga kananan hukumomi 26 suka halarci taron da aka gudanar a dakin taro na Sir Ahmadu Bello dake cikin sakatariyar jihar jigawa.
Usman Mohammed Zaria
-
Labarai3 days agoIran ta Tabbatar da Kisan Ayatollah Khamenei a Hare-haren Amurka da Isra’ila
-
Labarai4 days agoMajalisar Dokokin Jihar Kaduna Ta Amince da Kasafin Kudin Kananan Hukumomin Jihar na 2026
-
Labarai5 days agoAzumin Ramadan: Shugaban Karamar Hukumar Birnin Kudu Ya Bada Tallafin Kudi ga Marasa Galihu
-
Labarai7 days agoUwargidan Gwamnan Zamfara Ta Kaddamar da Rabon Tallafin Ramadan ga Marasa Galihu
-
Labarai4 days agoBankin Raya Kasashen Afirka Zai Samar da Shirin Bunƙasa Aikin Noma a Jigawa
-
Labarai6 days agoWani Bam Kirar Hannu Ya Fashe a Kan Hanyar Gusau Zuwa Funtua
-
Labarai1 day agoGwamna Namadi Ya Raba Tallafin Ramadan ga Ma’aikata da Marasa Galihu
-
Labarai14 hours agoHukumar Kula da Kogin Benuwe ta Dauki Matakin Yashe Laka da Yashi da ke Barazana ga Noman Rani
