Labarai
Hukumar Alhazai Ta Birnin Tarayya Ta Bai Wa Alhazai Zabi
Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Babban Birnin Tarayya Abuja ta bukaci maniyyatan da ke son a mayar musu da kudaden aikin Hajji da suka biya sakamakon karin da aka yi, da su gabatar mata da bukatar hakan.
Jami’in Hulda da Jama’a na Hukumar Muhammad Lawal Aliyu ne ya sanar da hakan a wata sanarwa da ya rabawa manema labarai.
Muhammad Aliyu ya ce Maniyyatan da suka riga suka biya Nera Miliyan Hudu da Dubu Dari Shida da Casa’in da Tara, za su cikasa Nera Miliyan Daya da Dubu Dari Tara da Goma sha Takwas nan da ranar 27 ga watan Maris 2024, domin samun damar gudanar da aikin Hajjin.
Hakan a cewarsa ya yi daidai da sabon umurnin da Hukumar Alhazai ta Kasa ta bayar.
“Don haka dukkan maniyyatan da suka riga suka biya kudi a baya, za su kara biyan kumanin Nera Milyan Biyu, yayin da wadanda ba su biya ko sisi ba, za su biya jimillar Nera Miliyan Takwas da Dubu Dari Biyu da Hamsin da Hudu kafin cikar wa’adin. “Inji shi.
Hukumar ta shawarci wadanda ke son a mayar musu da kudadensu da su rubuta bukatar hakan ga Daraktan hukumar ta babban birnin tarayya Abuja tare da bayanan asusun ajiyarsu na banki domin a dawo musu da kudaden, ko kuma su dage tafiyarsu zuwa shekara mai zuwa.
-
Ilimi6 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai5 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
-
Labarai1 day ago
Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu
-
Labarai1 day ago
NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta
