Labarai
Matashiya Ta Harbe Kanta A Ofishin ‘Yan Sandan Amurka
Wata budurwa ta harbe kanta har lahira da bindiga mallakar maitaimakin babban sufeton ‘yan sanda a harabar wani ofishin ‘yan sanda da ke California.
Matashiyar, wacce ba a bayyana sunanta ba, ta isa wurin ne inda ta fara buga kofar ofishin na ‘yan sanda da ke kusa da birnin Los Angeles.
Yayin da jami’an suka je bude kofa, matashiyar ta yi nasarar kwace wata bindiga daga daya daga cikinsu.
A cikin wata sanarwa fa ya fitar, Ofishin ‘yan sanda na gundumar Los Angeles ya ce “matashiyar ta kutsa cikin harabar ofishin ne inda ta kai hannun ta kwato bindigar mataimakin sufeton.”
Sanarwar ta ci gaba da cewa, an yi gwagwarmaya tsakanin mataimakan sufeton da matashiyar da ta yi nasarar zare masa bindiga, inda ya yi kokarin kwacewa.
A lokacin gwagwarmaya, matashiyar ta raunata kanta da bindiga,inda ta mutu nan take a cewar ma’aikatan lafiya da suka isa wurin.
Jami’an ke bincike sun ce sun fara binciken ne biyo bayan kiran iyayen matashiyar wadanda suka rene ta, inda suka kira don ba da rahoton cewa tana fama da matsalar tabin hankali.
-
Ilimi6 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai5 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
-
Labarai21 hours ago
Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu
-
Labarai23 hours ago
NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta
