Connect with us

Labarai

Hukumar Alhazai Ta Birnin Tarayya Ta Bai Wa Alhazai Zabi

Published

on

Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Babban Birnin Tarayya Abuja ta bukaci maniyyatan da ke son a mayar musu da  kudaden aikin Hajji da suka biya sakamakon karin da aka yi, da su gabatar mata da bukatar hakan.

Jami’in Hulda da Jama’a na Hukumar Muhammad Lawal Aliyu ne ya sanar da hakan a wata sanarwa da ya rabawa manema labarai.

Muhammad Aliyu ya ce Maniyyatan da suka riga suka biya Nera Miliyan Hudu da Dubu Dari Shida da Casa’in da Tara, za su cikasa Nera Miliyan Daya da Dubu Dari Tara da Goma sha Takwas nan da ranar 27 ga watan Maris 2024, domin samun damar gudanar da aikin Hajjin.

Hakan a cewarsa ya yi daidai da sabon umurnin da Hukumar Alhazai ta Kasa ta bayar.

Don haka dukkan maniyyatan da suka riga suka biya kudi a baya, za su kara biyan kumanin Nera Milyan Biyu, yayin da wadanda ba su biya ko sisi ba, za su biya jimillar Nera Miliyan Takwas da Dubu Dari Biyu da Hamsin da Hudu kafin cikar wa’adin. “Inji shi.

Hukumar ta shawarci wadanda ke son a mayar musu da kudadensu da su rubuta bukatar hakan ga Daraktan hukumar ta babban birnin tarayya Abuja tare da bayanan asusun ajiyarsu na banki domin a dawo musu da kudaden, ko kuma su dage tafiyarsu zuwa shekara mai zuwa.

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Labarai

Labarai20 hours ago

Amurka Ta Dakatar Da Kudurin Kai Jirgin Bama-Bamai Zuwa Isra’ila

Amurka ta sanar da batun dakatar da shirin ta na kai jirgi dauke da bamabamai zuwa Israila a cikin makon...

Labarai20 hours ago

NAHCON Ta Jinjinawa Hukumar Alhazai Ta Jihar Jigawa Bisa Shirye-shiryen Hajjin Bana

Darakta Janar na Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Jigawa Alhaji Ahmed Umar Labbo ya karbi tawagar gani da ido...

Kasuwanci2 days ago

CBN Ya Bai Wa Masu POS Wa’adin Yin Rajista Da Gwamnati

Babban Bankin Najeriya CBN ya bayar da wa’adin ranar 7 ga watan  Yulin 2024 ga masu POS su kammala rajista...

Fasaha2 days ago

Kusan Malaman Makaranta Dubu 2 Ke Samun Horo a Barno

  Gwamnatin jihar Borno ta fara aikin horas da malamai 1,949 a matakin farko da aka gano cewa suna iya...

Fasaha2 days ago

Bankuna Za Su Fara Cirar 0.5% Daga Masu Tura Kudi Ta Intanet

  Babban Bankin Najeriya (CBN) ya umurci bankunan kasar su fara cirar kaso 0.5 cikin 100 na duk kuɗin da...

Labarai2 days ago

An kashe Falasɗinawa 34,800 tun fara yaƙi – Ma’aikatar lafiyar Hamas

Ma’aikatar lafiya ta Hamas a Gaza ta ce an kashe Falasdinawa 34,789 a yankin tun ranar 7 ga watan Oktoba,...

Ilimi5 days ago

Gwamnatin Jigawa Za Ta Samar Da Gidaje A Jami’ar Tarayya Da Ke Babura

Gwamnatin jihar Jigawa ta ce za ta ci gaba da tallafawa harkokin koyo da koyarwa a Jami’ar Fasaha ta Gwamnatin...

Labarai5 days ago

An Samar Da Sabon Tsari Da Zai Inganta Harkar Noman Rogo A Najeriya

Shugaban kungiyar masu noman rogo ta Najeriya (NCGA), Mustapha Othman Bakano, ya kaddamar da wani tsari na samar da kasuwa...

Labarai7 days ago

Gwamnatin Jigawa Za Ta Samar Da Tarakta 300 Ga Manoma Daga Amurka

A kokarinta na ci gaba da habbaka harkokin noma, Gwamnatin Jihar Jigawa ta ƙulla wata yarjejeniyar haɗin gwiwa da wasu...

Labarai7 days ago

An kama masu zanga-zanga 17 a jami’ar Texas

An sake kama ƙarin mutanen da ke da alaƙa da zanga-zangar nuna goyon baya ga Falasɗinawa inda a wannan karon...

Mafi Shahara