Kasuwanci
Gwamna Namadi Ya Sha Alwashin Kara Inganta Kasuwar Maigatari
Gwamnatin Jihar Jigawa ta tabbatar wa al’ummar ƙaramar hukumar Maigatari cewa kasuwar Maigatari za ta zama ɗaya daga cikin cibiyoyin kasuwanci a Najeriya.
Gwamna Umar Namadi ne ya bayar da tabbacin yayin da yake jawabi a taron sauraron jama’a da aka gudanar a Maigatari.


A cewarsa, jihar tana aiwatar da jerin ayyuka da nufin bunƙasa harkokin kasuwanci da kuma samar da ayyukan yi ga matasan da ba su da aikin yi.
Gwamnan ya duba aikin ginin ɗakin taro da shugaban ƙaramar hukumar Maigatari, Alhaji Muhammad Na’Allah ke yi, inda ya yaba wa shugaban ƙaramar hukumar Maigatari bisa aiwatar da manyan ayyuka.


Gwamna Namadi ya kuma kaddamar da ginin ajujuwa uku na makarantar firamare da ɗan majalisar tarayya mai wakiltar Gumel, Maigatari, Sule Tankarkar da Gagarawa, Nazifi Sani, ya gina a garin Maigatari.
Ya ƙara bayyana godiya ga jama’ar Maigatari bisa kyakkyawar karɓar da suka yi masa tare da tawagarsa a lokacin ziyarar.


Rediyon Najeriya ya ruwaito cewa, Gwamna Malam Umar Namadi ya tarbi ‘yan adawa sama da dubu biyu da suka canza sheka zuwa jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a yankin.
Usman Muhammad Zaria
-
Ilimi6 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
-
Labarai1 day ago
Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu
-
Labarai1 day ago
NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta
