Kasuwanci
Shugaban Radiyon Najeriya Kaduna Ya Yi Babban Taron Farko Da Sashen Yada Labaran Gidan

An gudanar da taron farko tare da sabon Daraktan Shiyya na Rediyon Najeriya Kaduna, a ranar Laraba, 10 ga Satumba, 2025.
Taron wanda aka fara shi da karfe 10 na safe, ya samu halartar dukkan ma’aikatan gudanarwa na sashen da sauran ma’aikatan.
Da yake jawabi ga ma’aikatan, Daraktan shiyya na FRCN Kaduna, Malam Haruna Idris ya bayyana fifikon sa ga labarai, inda ya jaddada cewa ba za a amince da sakaci a bakin aiki ba, sannan ya yi gargadi kan rashin da’a.

Ya nuna rashin jin dadinsa game da rashin tsaftar muhalli tare da yin kira da a sauya hali ta hanyar yin abin da ya dace.
Ya bayyana cewa kowa na da rawar da zai taka, don haka akwai bukatar a hada kai, ya kara da cewa ba zai lamunci munanan dabi’u ba.
Bugu da kari, Idris ya gargadi dukkan ma’aikata game da lokaci, yana mai nuni da cewa za a yi wa wadanda suke gaza cika alkawuran da suka dauka na zuwa aiki akan lokaci domin za a hukunta duk wanda ya aikata ba daidai ba
A cewarsa, ya shafe shekaru sama da ashirin da biyar yana aikin jarida, inda ya jaddada kudirinsa na sauya fasalin dakin labarai da ma Radio Nijeriya baki daya.

Malam Haruna Idris ya ba da umarnin cewa daga yanzu dole ne labarai su samar da ingantattun abubuwa na tsawon mintuna ashirin da biyar domin ci gaba da martabar gidan Rediyon Najeriya Kaduna.
Daraktan shiyyar ya shawarci ma’aikatan Labarai da al’amuran yau da kullum da su jajirce wajen gudanar da ayyukansu yadda ya kamata bisa ka’ida da ka’idojin aiki.
Idris ya sanar da cewa babban taron zai kasance duk wata, daga yanzu, ya kara da cewa halartar taron ya zama tilas ga kowane ma’aikaci kuma ya yi gargadin makararru.

“Idan na ce karfe 10 na safe, ina nufin karfe 10 na safe, don haka dole ne kowa ya kasance a kan lokaci a duk lokacin da na kira taro. A kan abubuwan da ke cikin labarai, a koyaushe ina sauraron labarai, saboda haka, dole ne kowa ya kasance da gaske ga abin da yake yi.
Tun da farko a jawabin bude taron mataimakin daraktan yada labarai (DDN) Aminu Abdullahi Gombi ya jaddada bukatar dukkan ma’aikatan su jajirce wajen gudanar da ayyukansu.
Ya koka akan mummunar dabi’ar nan ta rashin da’a tare da yin kira da a canza dabi’u, sannan ya bukace su da su tashi tsaye domin marawa Daraktan shiyya baya domin cimma burinsa na kawo sauyi a tashar.
Alhaji Haruna Idris ya kara jaddada aniyarsa ta magance kalubalen da Radio Nijeriya Kaduna ke fuskanta da yardar Allah, sannan ya nemi shawarwari masu kyau da za su ciyar da tashar gaba.
Sai dai ya yi alkawarin yin adalci ga kowa ba tare da la’akari da bambance-bambance ba.
Cov/ Sani Sulaiman
-
Labarai3 days agoIran ta Tabbatar da Kisan Ayatollah Khamenei a Hare-haren Amurka da Isra’ila
-
Labarai4 days agoMajalisar Dokokin Jihar Kaduna Ta Amince da Kasafin Kudin Kananan Hukumomin Jihar na 2026
-
Labarai4 days agoAzumin Ramadan: Shugaban Karamar Hukumar Birnin Kudu Ya Bada Tallafin Kudi ga Marasa Galihu
-
Labarai6 days agoUwargidan Gwamnan Zamfara Ta Kaddamar da Rabon Tallafin Ramadan ga Marasa Galihu
-
Labarai6 days agoWani Bam Kirar Hannu Ya Fashe a Kan Hanyar Gusau Zuwa Funtua
-
Labarai3 days agoBankin Raya Kasashen Afirka Zai Samar da Shirin Bunƙasa Aikin Noma a Jigawa
-
Labarai3 days agoGwamnatin Jigawa ta Gargadi ‘Yan Kwangila Kan Ingancin Abincin Ramadan
-
Labarai3 days agoMasarautar Hadejia ta Raba Zakkar Kayan Amfanin Gona da Dabbobi a Garin Unik
